FIFITA TSAKANIN KISHIYOYI HARAMUN NE !!!



FIFITA TSAKANIN KISHIYOYI HARAMUN NE !!!

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum.
Malam na kasance ina kyautata Ma mijina iya gurgwadona,to amma matsalan bani kadai bace sai yakasance nima yanamun duk wani Abu najin dadi da kyautatawa fiye da kishiyar tawa wani Lokacimma baya Boyewa to shin malam bama Shiga hakkinta. Menene hukuncin haka. 
Nagode

*AMSA*👇

Wa alaikum assalam
Ya wajaba ayi adalci a lamura na zahiri (kamar abinci, tufa) tsakanin kishiyoyi, Annabi SAW yana cewa: "Duk Wanda yake da mata biyu, amma bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar alkiyama sahensa daya a shagide".
Ya halatta in kana da mata guda biyu ka fi son daya daga ciki, ka fi jin dadin saduwa da ita, ka fi dadewa a dakinta, Annabi SAW ya fi son nana Aisha akan duka matansa tara da ya mutu ya bari, kuma matansa da sahabbansa sun san hakan, kamar yadda ya tabbata a sahihul Bukhari.

Allah ne mafi sani 

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)