HUKUNCIN AUREN NAMIJIN DA BAYA HAIHUWA



HUKUNCIN AUREN NAMIJIN DA BAYA HAIHUWA

*TAMBAYA*❓

Aslm Alkm malam Don Allah Ya halarta auren namijin da baya haihu koma iyayenta sunsan da haka baya haihu.

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu. Alhamdu lillahi rabbil aalamin wassalatu wassalamu alaa rasulillah wa alaa aalihi wa sahbihi ajma'in wa man waalaahu.

Ya halatta mace ta auri namijin da baya haihuwa, amma idan da sanin ta kuma da zaɓin ta ko yardar ta. Abin da yake bai halatta ba, shine waliyyin ta ya tilasta mata auren shi alhali bata son shi, ko kuma ba tare da sanin baya haihuwa ba.

Amma Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya kwaɗaitar kan auren mai haihuwa, yace ku auri mata masu haihuwa, 

2940 - «تزوجوا الودود الولود فإني مكاثر بكم» .

(صحيح) ... [د ن] عن معقل بن يسار. الإرواء 1784.


Dalili haka shine, daga cikin manufofin aure, akwai yawaita al'ummar Annabi, hakan kuma ba zai samu ba har sai mun hayayyafa, sannan Annabi yayi alfahari da mu.

Wallahu ta'aala a'lam.

 *~_Amsawa_~* :-
 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)