HUKUNCIN HADASI



HUKUNCIN HADASI:

https://chat.whatsapp.com/Dv6jmbFbNBd3qcd41OWH2k

*TAMBAYA TA 160*
 
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.
Malam, na kasance idan wasanni sun auku a tsakanina da mijiina ko kuma idan tunani ya kama ni, sai wani ruwa mai yauƙi ya riƙa fito mini, to wai sai na yi wankan tsarki idan hakan ya faru?

 *AMSA A160:* 

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Abin da kike gani É—aya ne daga cikin abubuwan da suke janyo hadasi ga mutane idan sun fito musu:

[1] Akwai masu fitowa daga kowane irin mutum namiji ko mace, kuma babba ko ƙaramin yaro, su ne:
Tusa da kashi, da suke fitowa ta dubura.
Fitsari wanda ke fitowa ta gaba.
Hukuncinsu: Kowannensu najasa ne. Dole ne a wanke inda suka fito kawai, a sake alwala. Wurin da suka shafa kuma dole sai an wanke shi da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa. Sai dai fitsarin jariri a kan tufa, shi ba sai an wanke ba. Idan aka jiƙa tufar da ruwa kawai ya wadatar.

[2] _Sai kuma waÉ—anda suke fitowa daga manyan mutanen da suka balaga, su ne: Wadiyyi da maziyyi da maniyyi._

*Wadiyyi:* Ruwa ne fari mai kauri da yake fitowa yawanci a ƙarshen fitsari. Kuma yana fitowa yawanci daga tsofaffi ne. Hukuncinsa iri ɗaya da na fitsari ne: A wanke inda ya fito da inda ya taɓa kawai, a sake alwala.

*Maziyyi*: Ruwa ne tsararo mai yauÆ™i, yana fitowa a lokacin Æ™aramar sha’awa, kamar a lokacin tunani a kan sha’anin jima’i, ko kallon sha’awa ga al’aurori, ko wasannin sha’awa a tsakanin miji da mata. Ba ya tunkuÉ—ar juna wurin fitowarsa, yawanci ba a ma ji ko sanin fitowarsa sai dai a ga jiÆ™ewa kawai. Hukuncinsa shi ne: Shi najasa ne, don haka sai a wanke duk inda ya shafa da dukkan al’aurar da ya fito daga cikinta, sannan kuma a sake alwala. Idan ya shafi tufafin matasa an yi sassauci cewa a jiÆ™a wurin da ruwa kawai maimakon wankewa.

*Maniyyi*: Ruwa ne fari mai kauri (a wurin namiji), yana tunkuÉ—ar juna a lokacin fitowarsa, kuma yana janyo sakewar jiki bayan fitowarsa. Yana fitowa ne a lokacin babbar sha’awa, kamar a lokacin saduwar jima’i, ko wasa da gaba (istimna’i). Yakan fito a cikin barci kamar yadda yake fitowa a farke. Hukuncinsa: Ba najasa ba ne a maganar da ta fi Æ™arfi a wurin malamai. Amma kuma yana wajabta yin wankan da ake kira wankan janaba a bayan fitowarsa.

[3] _Akwai kuma waÉ—anda suke fitowa ta gaban manyan mata kaÉ—ai su ne: Haila da nafasi da kuma istihala._

*Haila*: Jini ne da yakan fita daga gaban mace a lokacin da ta balaga, ba don wani dalili na rashin lafiya ko wata larura ba. Jini ne na al’ada, wanda ba shi da wani iyakantaccen adadi ta fuska yawa ko kwanaki. Yana maimaita fitowa yawanci a kowane wata guda ne. Hukuncinsa: Mai haila ba za ta yi sallah ba, ba za ta yi azumi ba, ba za ta yi É—awafi ba, ba za a sadu da ita ba, kuma ba za a sake ta ba. Bayan É—aukewarsa wajibi ne ta yi wankan da ake kira wankan haila. Tana rama azumman da ba ta yi ba a lokacinsa, amma ba za ta rama sallolin ba.

*Nifasi*: Jini ne da ke fitowa saboda dalilin haihuwa. Mafi yawan kwanakinsa kwana arba’in ne saboda hadisi sahihi da ya zo a kan haka. Don haka, idan ya kai kwana arba’in sai mace ta yi wanka, ta cigaba da sallah, da sauran ayyukan ibada. Haka ma idan ya É—auke kafin cikan kwanaki arba’in É—in. Hukuncinsa daidai da haila ne.

*Istihaala*: Jini ne da yakan fita a dalilin wata matsala ta rashin lafiya a cikin mace. Yakan zama ya karu a kan adadin kwanankin haila a wurin mace. Hukuncinsa: Ba ya hana komai daga cikin abubuwan da haila ko nifasi ke hanawa. Sai dai dole ne mai Istihaala ta sake alwala ga kowace sallah. Kuma tana iya yin wanka ta haÉ—a salloli biyu da suka haÉ—a lokaci: Azahar da La’asar ko Maghriba da Isha’.

[4] *Daga cikin waɗannan matsalolin, duk wanda ya janyo wanka kafin a samu tsarki, kamar fitar maniyyi ko haila ko nifasi, shi ne ake kira: Babban Hadasi. Wanda kuma ya janyo alwala, kamar fitar fitsari ko kashi ko maziyyi da sauransu shi ne: Ƙaramin Hadasi.*

[5] _Kuma waÉ—annan abubuwa suna zama hadasi ne kaÉ—ai idan sun fito ta fuskar lafiya ta hanyar da aka saba, amma duk lokacin da suka fito ta fuskar rashin lafiya, kamar idan suka wuce iyaka a wurin yawa da lokacin fitarsu, to sun zama larura. Kuma ba za su hana komai ba na sallah ko azumi ko É—awafi da sauransu._
Wal Laahu A’lam.

Wa Sallal Laahu Wa Sallama Alaa Nabiyyinaa Muhammadin Wa Alihi Wa Sahbih.
*_Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy._*
Post a Comment (0)