HUKUNCIN KARI KO RAGI A CIKIN AL'ADA.
;
*TAMBAYA*❓
;
ASSALAMU ALAIKUM, da fatan mallam yana cikin koshi lfy,. dan ALLAH mal ina da tambaya, ni ce nake jinin haila kwana 5 na saba yi to amma wannan karan kwana 9 yayi min, bayan na yi wanka da kwana 3 sai kuma wani brown din abu tare da jini kaÉ—an yake fito min wanda har yanzu bai dena ba shi ne nake tambaya akan hukuncin wannan rikitaccen lamarin nawa. Nagode
:
*AMSA*👇
:
To malama ana iya samun ragi ko kari a jinin haila, don haka karin ba zai cutar ba, saboda shi ma haila ne, mutukar bai wuce iyaka ba, ta yadda zai zama jinin istihala, amma brown din da kike gani to mutukar bayan kin kammala haila ya zo, to ba ya cikinta, ba zai hana azumi ba da sallah, domin shi ne ake kira kudra, ita kuma kudra, idan ta zo bayan jinin haila, to ba ta cikinsa, kamar yadda hadisin Ummu Addiyya ya yi nuni, inda take cewa: "Mun kasance ba ma kirga kudra da sufra bayan tsarki a cikin haila.
Bukhari 1\426
Allah ne mafi Sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177