HUKUNCIN ZAMA DA MIJI MAI KAKKAUSAN HALI



HUKUNCIN ZAMA DA MIJI MAI KAKKAUSAN HALI :
:
*TAMBAYA*❓
:
Salamun alaikum Malam
Don Allah meye addini yace game da Mijin da ya Kira matarsa ya zage ta sannan yace ta tafi gidansu se ya nemeta, kuma ba laifin da tayi masa. Iyakaci kawai in ta nemi ya saurareta yaki in ta masa text bayaso.
Sannan Bata tafi ba, Amma yaki Bata kudin cefene yaci gaba da bawa kishiyarta, sannan ta zo ta bashi Hakuri yaki sauraranta Sati biyu baya Mata magana.
:
AMSA
:
Wa alaikis salam wa rahmatullahi
Irin wannan babu adalci aciki. Mutukar dai yadda kika faÉ—a din haka akayi, to ya zalunceta, ya shiga hakkinta, kuma bai yi koyi da sunnar Manzon Allah ï·º acikin wannan ba.
Allah Madaukakin Sarki ya fada acikin suratun Nisa'i ayah ta 19 cewa :
"KU ZAUNA DASU TARE DA KYAUTATAWA".
Al Imam Ibnu Katheer da yazo kan fassarar ayar sai yace : "Wato ana nufin kuyi musu zance mai daÉ—i, kuma ku kyautata ayyukanku (garesu) da siffofinku ga matayenku gwargwadon ikonku kamar yadda kuke so su aikata hakan gareku.".
Sannan ya kawo hadisin Annabi ï·º inda yake cewa : "Mafificinku, shine wanda yafi aikata alkhairi ga iyalansa. Ni nafiku aikata alkhairi ga iyalaina".
Ibnu Katheer yace "Yana daga cikin halayen Manzon Allah ï·º cewa shi mai kyawun zamantakewa ne, kuma mai dawwamammen murmushi ne (wato ba ya murtuke fuska ga iyalansa) yana yin wasa da iyalansa, kuma yana jansu ajikinsa. Yana yalwata musu abincinsu kuma yana yi musu abinda zai sanya suyi dariya."
To amma waÉ—annan abubuwan da kika zayyana na halayen mijinki, sunyi muni kwarai. Ina baki shawarar cewa kici gaba da bin umurni tare da kyautata masa koda kuwa shi ya munana miki. Kada ki rama abinda yake miki. Ki yafe masa kiyi masa addu'a ki roki Allah ya shiryeshi.
Aurenku yana nan tunda bai ce ya sakeki ba. Amma laifin rashin adalcin nan kuma yana nan akansa. Tunda Manzon Allah ï·º yace "Duk wanda ya kasance yana da mata biyu, sai ya karkata zuwa ga É—ayar cikinsu, to zai zo aranar Alkiyamah tsagin jikinsa ya karkace wato ya shanye kamar na paralysis.

Wallahu A'alam

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)