HUKUNCIN KIRAN WANI KO SIFFANTA WANI DA SUNNAH ALLAH



HUKUNCIN KIRAN WANI KO SIFFANTA WANI DA SUNNAH ALLAH
:
*TAMBAYA*❓
:
Naga wasu daga cikin sunayen Allah idan za'a Kira mutum da shi sai ace Abdullahi Abdurrazak amma kuma wasu ba'asa abdu ɗin kamar basiru, nafiu, auwalu. dadai sauransu to hakan ya hukuncin yake ?
:
*AMSA*👇
:
Toh abayacan inaganin munyi cikakken bayani gameda sunayen Allah harma awata munasabar muka kasa sunayen Allah din kashi biyu mukace akwai sunayen Allah wadanda lafazinsu haramunne akira wani da wannan lafazin wanda ba Allah ba kamar Allahu da Arrahmanu kaga wadannan sunan haramunne a kira wani dasu ko a siffanta wani dasu komai girmanshi su waɗannan biyun sun ke6anta ga Allah ne shi kadai. Amma sunayenda ba waɗannan ba yana iya yiwuwa akira wani dasu amma be isaba yasamu cikakken kamalarsu, Allah shi nashi sunayen da siffofin cikakkune kuma kammalallu. Wannan yasa har kaji Allah ta'ala dakansa acikin Alqur'ani ya siffanta wasu da irin abinda ya siffanta kanshi dasu. Kamar Al'arshi Allah yakirashi Al-Azeem, awani wajan kuma Alkareem. Hakama Annabi (s.a.w) ankirashi Ra'ufur Rahim bayan kuma dukansu sunayen Allah ne toh shine yasa malamai se suka kasa sunayen iri biyu wato akwai waɗanda ana iya kiran wani dasu sedai basuda kamala se a haqqin Allah, akwai waɗanda sukuma ana iya siffanta wani dasu, amma kuma suma ɗin ba kowanne sunan Allah bane yake halasta akira mutum dasu kamar Allahu Arrahmanu da Arrahimu wannan ba,a kiran wani dasu. Amma kamar Albasiru ko Aljamilu ko Al-Auwalu da ire iren wadannan duk ana iya kiran wani dasu amma suma ɗin akwai Abdul din kaine zaka qaddarashi duk inda kaji Basiru toh Abdul Basirune aka share Abdul ɗin, hakama Jamilu dasu Nafi'u. Amma shikuma Auwalu inkaji wannan toh Muhammadu zaka Qaddara masa wato Muhammadul Auwal shine se ake goge Muhammad din ace Auwal kawai ko Muhammadus Sani sekaji ance sani. Amma idan ka duba littafan tafsiri wajan karkashin Hal ta'alamu lahu samiyya zakaji bayananda malaman sukayi.

Allah Yasa mudace

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

1 Comments

  1. An unique and detailed evaluation of the 3D Printing Service Bureaus market examines the competitive changes and progress in the course of the forecast interval. The crucial elements of the product are examined Portable Washers for investment alternatives and policies that help the product and its 3D Printing Service Bureaus market. The study consists of the demographics, new merchandise, different service choices, market development methods, dangers, challenges, and investment alternatives. The present economic scenarios estimate the market projection for the forecast interval.

    ReplyDelete
Post a Comment