ZAKKAR NOMAN RANI



ZAKKAR NOMAN RANI

TAMBAYA❓

Assalamu alaikum, Malam Dangane da zakkar amfanin gona da ka noma ta hanyar noman rani da aka yi amfani da ban ruwa na inji kuma da akayi lissafin abinda aka kashe sai ya zama kayan da aka samu bai biya kudin wahalarsa ba, yaya zakkarsa zata kasance?
Allah ya kara budi!

*AMSA*👇

Wa'alaikum assalam, duk da haka za'a bada zakkarsa mutukar ya kai Sa'i 300.
Za'a fitar da daya bisa ashirin, 1/20 na abin da aka samu, wato in Sa'i dari uku ne sai a bayar da Sa'i sha biyar, in dari hudu ne sai a bada Sa'i ashirin، kamar yadda hadisin Buhari mai lamba ta: 1483 ya nuna hakan.
In har bai kai wancan mikdarin ba to babu zakka a ciki.

Shari'a ta rataya zakkar kayan amfanin gona ne da samun Sa'i dari uku, Hakan kuma ba Shi da alaka da faduwa ko samun riba a noman.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)