HUKUNCIN YIN SALLAH A ZAUNE



HUKUNCIN YIN SALLAH A ZAUNE

*TAMBAYA*❓

Assalammu Alaikum, dan Allah mene ne hukuncin me yin sallah a zaune, kuma tana yawo ko ina amma idan ta zo yin sallah sai kafan ya fara zafi sai ta yi a zaune?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salamu, sallar farilla wajibi ne a yi ta a tsaye, saboda yin sallah a tsaye rukuni ne daga cikin rukunnan sallah, ba makawa sai mutum ya yi ta, amma yin sallah a zaune ga wanda ba shi da lafiya, ko ba shi da ikon yin tsayuwar, wannan babu laifi idan ya yi sallah a zaune, saboda ya tabbata daga sahabin Annabi ï·º Imrana É—an Husaini Allah ya qara masa yarda ya ce:
Na kasance ina fama da basir, sai na tambayi Annabi ï·º game da yadda zan yi sallah, sai ya ce mani: "Ka yi sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba ka yi a zaune, idan ma ba za ka iya ba ka yi a kan É“arin jikinka (wato a kwance)". Bukhariy 1117.
Wannan dalili ne a kan yin sallah a zaune ga mara lafiyan da ba zai iya yin ta a tsaye ba, ko kuma ga wanda tsayuwar take masa tsananin wahala kamar wanda ya tsufa tukuf da makamantan haka. Amma lafiyayyen mutum, wanda yake da ikon yin sallah a tsaye, idan ya yi ta a zaune sallarsa ba ta inganta ba.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


*_Yadda Ake Hadin Dayake Magance Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada_*


Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Garin gauta 
* Tsamiya
* Zuma
*Bayani;* Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki gauraya ki tafasa ki tace zuwan ki zuba zuma ki juya ki dunga sha.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da suke, ta wa'innan numba;* 👇 👇 👇

08162268959,08038902454
Post a Comment (0)