MATSAYIN RUFE QAFAFU A CIKIN SALLAR MACE



MATSAYIN RUFE QAFAFU A CIKIN SALLAR MACE

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu. Ina wuni Malam fatan ka wuni lafiy. Ya hakuri da mu. Allah ya saka da alhairi. Allah ya qara illimi mai amfani da albarka. Hukuncin rufe kafa yayin Sallah. Na ji wasu sun ce idan ba'a rufe ba. To wai Sallah ba ta Inganta ba.

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salám, malamai sun yi saɓani game da hukuncin rufe qafafun mace mai sallah, ta inda mafi yawan malaman Musulunci suke da fahimtar suturta qafafu ga mace mai sallah wajibi ne, saboda mace gaba ɗayanta al'aura ce in banda fuska da tafukan hannu. Wannan ita ce fahimtar maz'habar Malikiyya da Shafi'iyya da Hanabila. Amma su Hanafiyya suna da fahimtar cewa rufe qafafu ga mace a lokacin sallah ba wajibi ba ne saboda a wurinsu qafafu ba al'aura ba ce.
Duba Almausu'atul Fiqhiyya (7/85)
Saboda haka ne mafi yawa daga cikin malamai suka ce idan mace ta yi sallah alhali qafafunta a buÉ—e sai ta sake yin wata sallar matuqar lokacinta bai wuce ba, amma sallolin da lokacinsu ya wuce ba za ta rama su ba saboda uzurin rashin sani.
Abin da ya fi dacewa shi ne mace ta fita daga cikin saɓanin malamai ta riqa rufe qafafunta a duk sallar da za ta yi, sallolin da ta yi a baya kuma ba sai ta rama su ba saboda a lokacin ba ta sani ba.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)