INA HUKUNCIN, WANDA BAYA WASA DA GABANSA, AMMA IN SHA'AWA TA DEBE SHI YANAYI DA PILLOW??
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum To malam inada tambaya shi wanda ba wasa yakeyi da alaurarsa ba amma idan yaji sha'awa to xai kwanta katifa yakama yi kamar yana saduwa da mace sai ya kawo to menene hukuncin wanan malam
Sannan kuma idan mutum ya kalli fina finan batsa ya kawo to wanan istimnai ne?
:
*AMSA*👇
:
Wa,alaikumussalam eh duka sun shiga cikin haramcin domiN ALLAH ya haramta yin hakan, yakuma kira duk masu aikata irin haka da Qetare iyaka.
Sannan manzon ALLAH yayi kira ga matasa da suyi Aure in sunada hali in babu suyi azumi dan zai zama musu kariya.
Amma fa auren shine dai dai dan azumin kaÉ—an yake ragewa.
Idan kuma ka fitar da maniyii wanka ya kamaka dole.
Da wannan muke kira dan ALLAH a taimaka a samari da 'yan mata suyi ma yayan su Aure, idan fa suka lalace dukkan ku kunada laifi domin baku kula dasu ba.
ALLAH cewa yayi "ku tseratar da kanku da iyalanku daga wuta..."
kaidan kayi Aure É—an ka yakai shekara 23 ko sama da haka ko qasa da haka yace ma yanason Aure kai kuma kacemar saiyayi makaranta.
Ana samun matsala wai sai ace ai namijine kai, to idan ba'a barka kayi Auren ba ita macen wa zai Aure ta??
Dan ALLAH Kuji tsoron ALLAH ku taimakawa yaranku suyo Aure kar kuma kuyi musu Auren dole dan haramun ne.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::
_Dan uwanku a musulunci._
*MUHAMMAD AUWAL ABU JA'AFAR AL-POTISKUMAWI*
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177