KADA KA BAYYANAR DA ZUNUBANKA.



KADA KA BAYYANAR DA ZUNUBANKA.
-
"A musulunci babu kyau aikin saɓo, sannan kuma haramcin yana ƙarfafuwa ga waɗanda bayan sunyi aikin saɓon kuma suzo suna bayyanarwa da jama'a irin nau'in aikin saɓon da suka kasance suna aikatawa a ɓoye"
-
"Allah maɗaukakin sarki yana son idan bawansa ya saɓa masa kuma shi Allah ɗin ya rufa masa asiri akan hakan, sai shi wannan bawan ya tuba daga zunuban nasa ba tare kuma ya faɗawa kowa ba, amma mafi sharrin masu saɓo shine wanda zai aikata saɓon Allah, bayan kuma Allah ɗin ya rufa masa asiri, sai shi mutumin yazo yana bayyanarwa da jama'a aikin saɓon nasa, to haƙiƙa Allah baya son haka kuma baya yafiya akan hakan"
-
"Abu Hurairata Allah ya ƙara masa yarda ya ruwaito cewa, lallai Manzon Allah ﷺ, yace: haƙiƙa dukkanin al'umma ta ana yafe mata zunubanta saidai banda masu bayyanarwa, shine mutum ya aikata wani aiki a cikin dare, bayan Allah ya siturta shi, sai kuma bayan gari ya waye sai yace yakai wane! Haƙiƙa ni na aikata abu kaza da kaza a cikin dare, bayan kuma kwana yayi Allah yana siturta shi, sai ya wayi gari yana me warware rufin asirin da Allah yayi masa"
Sahih Muslim: 2990
-
Facebook page
https://mobile.facebook.com/Hausa-Islamic-Pictures-Quotes-304897013359792/?ref=opera_speed_dial_freefb
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
Post a Comment (0)