Budurwata Ba Ta Haila, Falalace Ko Matsala Ce?



Budurwata Ba Ta Haila, Falalace Ko Matsala Ce?

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum don Allah malam a taimaka min, matar da zan aura a yanzu haka auren bai fi wata biyu ba, shekararta 20 amma ba ta taba jinin haila ba. To malam wannan matsalace ko kuma falalace ? sannan kuma za ta iya haihuwa?.

*AMSA*👇

To dan’uwa tabbas haila tana daga cikin alamomin da suke nuna cewa mace za ta iya daukar ciki, kamar yadda wasu malaman tafsirin suka fada, wannan ya sa lokacin da za’a yiwa matar annabi Ibrahim bushara da haihuwa, sai da ta yi haila, saboda kasancewarta tsohuwa, haila kuma alama ce ta haihuwa, don haka duk matar da ba ta yin haila da wuya ta haihu, akan iya samun wasu matan ‘yan kadan wadanda suke iya haihuwa ko da ba su taÉ“a yin haila ba, saboda Allah mai iko ne akan komai. Abin da nake ba ka shawara shi ne ku je wajan likitoci, don su gwada ta, in har suka tabbatar ba za ta iya haihuwa ba, kana iya hakura da auranta, saboda haihuwa ginshiki ne, daga cikin ginshikan da suke sa ayi aure. Rashin yin haila ba falala ba ce, saboda hadisi ya tabbatar da cewa : “Haila jini ne da Allah ya hukuntawa dukkan ‘ya’yan nana Hauwa’u da jikokinta” kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba : 290. 

Allah ne mafi sani

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaÉ—a wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)