LADDUBAN ATISHAWA



LADDUBAN ATISHAWA

الحديث الحادي والثلاثون بعد المائة

في آداب العطاس

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: عَطَسَ رَجُلانِ عِنْدَ النبيِّ صلى الله عليه وسلم فَشَمَّتَ أَحَدَهُمَا وَلَمْ يُشَمِّتِ الآخَرَ، فَقَالَ الَّذِي لَمْ يُشَمِّتْهُ: عَطَسَ فُلانٌ فَشَمَّتهُ وَعطستُ أنا فَلَم تُشَمتني؟ قَالَ: إن هَذَا حَمِدَ الله، وإنَك لَمْ تَحْمَدِ الله.

أخرجه البخاري [6221]، ومسلم [2991] .


HADISI NA DARI DA TALATIN DA DAYA

LADDUBAN ATISHAWA

An ruwaito daga Anas bn Malik -Allah ya kara yarda a gare shi-, ya ce: Mutane biyu sun yi atishawa a wurin Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- sai ya yi addu'a wa daya daga cikinsu, bai yi wa dayan ba, Sai wanda ba a masa addu'ar ba ya ce:

Wannan ya yi atishawa sai ka yi masa addu'a, Ni kuma ba ka min addu'ar ba!

Sai ya ce:

"Lallai saboda wannan ya fadi kalmar godiya wa Allah (wato, ALHAMDU LILLAHI) Kai kuma baka fada ba".

Bukhariy [6221] ya ruwaito shi, da Muslim [2991].


FA'IDODI DAGA HADISIN

NA DAYA: Sunna ne idan mutum ya yi atishawa ya ce, ALHAMDU LILLAHI.

NA BIYU: Kuma mustahabbi ne mutum ya daga sautinsa a lokacin fadin hakan, saboda wadanda su ke kewaye da shi su ji shi, domin su yi masa addu'a.

NA UKU: Yin atishawa ni'ima ne daga ni'imomin Ubangiji ga bawa, sai ya dace a fiskanci ni'imar, da yin godiya wa Allah.

NA HUDU: Idan mutum ya yi atishawa ya ce: ALHAMDU LILLAHI, To sunna ne ga wanda ya ji shi, ya masa addu'ar neman rahama, da fadin: YARHAMUKALLAHU.

NA BIYAR: Idan mai atishawa bai ce *alhamdu lillahi* ba, to hakika bai cancanci ayi masa addu'a da Yarhamukallahu ba.

Allah ne Masani!

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)