HUKUNCIN MATAR AUREN DAKE SOYAYYA DA TSOHON SAURAYINTA



HUKUNCIN MATAR AUREN DAKE SOYAYYA DA TSOHON SAURAYINTA :

TAMBAYA TA 2362
********************
Assalamu Alaikum, Malam ya hidima da dalibai, Allah yasa ka da alkhairi, Malam wata tambaya ce dani, ina tare da wani saurayina Muna son juna sosai, to Allah cikin ikonsa baiyi aurena dashi ba sai da wani daban wanda azahirin gaskiya ba wani sonsa nake ba, yau shekarar mu 1 guda da auren amma har yau ban dena sonsa ba, har takai idan ina cikin bacin rai ko wata damuwa sai na kira shi naji muryarsa nakejin sauki, to Malam nasan hakan ba dai-dai bane, har addu'a nake akan Allah ya cire min sonsa a raina, amma na kasa na goge numban sa da duk abunda ya shafeshi, inason na fuskanci aurena na dena tunashi, Malam ina neman shawara me ya kamata nayi?.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Gaskiya shawarar da zan baki ita ce Kiji tsoron Allah ki gyara halayenki. Domin hakika Shaitan (La'ananne) ya riga ya Qawata miki Mummunan aiki amatsayin kyakkyawa. Ya mayar miki da Haram tafi soyuwa azuciyarki fiye da halal din ki.
Hakika yana daga cikin hakkokin Mijinki akanki cewa ki bashi dukkan kulawarki da duk wata soyayyar da zakiyi ma wani 'da namiji, da sha'awarki da duk wasu harkoki naki. To amma sai gashi shaitan ya dauki hankalinki ya dora bisa wani Qato chan awaje.
Ki sani Allah yana cewa : "KADA KU BIBBIYI SAWUN SHAITAN, DOMIN HAKIKA SHI MAKIYINKU NE MAI BAYYANAR DA KIYAYYA GAREKU".
Kuma Allah yace : "SHAITAN YANA TANADAR MUKU DA TALAUCI KUMA YANA UMURTARKU DA ALFASHA. ALLAH KUMA YANA TANADAR MUKU DA GAFARA DAGA GARESHI DA FALALA, KUMA ALLAH MAYALWACI NE MASANI".
Kiji tsoron Allah. Hakika wannan abinda kike ji din wato kururuwar shaitan ce. Da yawa wasu Matan auren da haka ne suke afkawa cikin zinace zinace. Daga karshe kuma su hadu da tozarta aduniya ga kuma azabar lahira mai tsanani tana jira.
Kiji tsoron Allah ki guje ma wannan shaitanin saurayin. Makiyinki ne ba masoyinki bane. Da ache masoyinki ne mai ya hanashi ya fito ya aureki?. Hakikar masoyinki na gaskiya shine wannan mijin naki da ya aureki ya rufa miki asiri.
Kiji tsoron Allah ki sani tsalle daya akeyi a afka ramin zina. Amma sai anyi shekaru dubunnai ana shan azaba acikinsa koda za'a fita.. Ki tuba ki koma ga Allah tun lokaci bai Qure miki ba.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)