Sahabbai: Katangar Karfe Gani Nan Bari Nan



Ramadaniyyat 1442H [15]

Dr. muhd Sani Umar ( Hafizahullah) 

Sahabbai: Katangar Karfe Gani Nan Bari Nan
_____________________________

1. Shi ya sa sukar shabban Annabi (ï·º) yake a makwafin sukar addini gaba daya, kuma magabata suka yi ittifaki kan cewa, su sahabbai ba sa jiran wani daga cikin wannan al’umma ya wanke su, watau ya ba da shaidar cewa su mutanen kirki ne, ta yadda ba za su zama adalai ba sai sun samu mai wanke su. A’a su ba sa bukatar haka, ba don komai ba, sai don Allah ya riga ya wanke su, ya yabe su a wurare daban-daban a cikin Alkur’ani.

2. Shi ya sa duk wanda zai zo yana sukar sahabin Annabi (ï·º), to addinin yake kokarin ya rusa, kamar yadda Abu Zur’a (R.H) yake cewa: “Idan ka ga wani yana sukar wani daga cikin sahabban Annabi (ï·º), to zindiki ne. Domin Manzo (ï·º) a wurinmu gaskiya ne, hakanan Alkur’ani ma gaskiya ne, kuma wadanda suka dauko mana Alkur’ani da sunnonin Annabi (ï·º) su ne sahabbai, saboda haka sai suke son su soki shaidunmu (watau sahabbai), amma su suka fi cancanta da a soka (ba sahabbai ba) kuma zindikai ne”. [Duba, Al-Khadib, Al-Kifaya, shafi na 49].

3. Zindiki shi ne wanda yake bayyana Musulunci a baki, amma a zuciyarsa ba Musuluncin yake yi ba. Wannan shi aka kira munafuki a cikin Alkur’ani; za su ce sun yi imani amma zukatansu ba su yi imani ba”, to shi ne malamai suke cewa zindiki.

4. Ya zo a cikin Tarikhu Baghdad na Alkhadibul Baghdadi [Juzu'i na 5, shafi na 505] cewa, a zamanin Haruna Rashid an zo da wani mutum daga cikin shugabannin zindikai ana kiran sa Shakir, don a yanke masa hukunci, sai ake tambayar sa, me ya sa kuke fara koyar da ‘ya’yanku kin sahabbai da akidar kore kaddara? Sai ya ce; “Abin da ya sa muke koya musu kin sahabbai shi ne, sahabban nan su ne suka yo dakon wannan shari’a, to idan muka rusa su, to mun rushe shari’ar gaba daya”. 

5. Don haka sahabbai katanga ce ta karfe mai karfin gaske wadda duk yadda mai son ya ga bayan Musulunci ko ya rushe shari'ar Allah, ko ya dagula wa Musulmi addininsu, hakarsa ba za ta cimma nasara ba, matukar wannan katanga na tsaye. Shi ya sa duk kokarinsu da karfinsu suke tattara shi wajen su ga sun rushe wannan katanga, sun kai ta kasa. To amma wannan aikin kawai ne ba zai taba nasara ba, saboda Allah ya yi alkawarin kare addininsa da daukaka shi, don haka su ma wadannan sahabbai ba za su gushe suna samin kariya daga Allah ba, ta hanyar masoya Allah da Manzonsa da addininsa.

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)