TAMBAYA
========
👇
Malam inawuni ya gida ya iyalai malam dan Allah ka temaka kamin rubutu akan wannan matsalar
Mijine bashida lpia antaba masa oparation har biyu daya apendix daya kuma tundaga farkon cikinsa zuwa mararsa aka bude yanzu a dinke yake malam yana yawan fama da ciwan ciki hassalima komai yaci wlhi seyayi kashin na da yake samun sukuni
Ga fama da matsalar basir in ya faramai jini yake zuba kamar anyanka abu
Malam yana da mata amman matar ma baya iya gamsar da ita yadda ya kamata se lokaci lokaci intayi sa'a
To malam ahakan yake neman aure matar ta fito ta fada masa se yace ahakan de zeyi auren sede ya mutu kuma itama amaryar sede tazo tayi hakuri da abunda ta samu
Kuma budurwa ze aura se yake cewa wai yadda ya saba mata haka zata hakura
Shin malam karin aurensa a musulunci ya hallatta shin inyayi auren bare shiga hakkin matarsa ba
Malam da matar take fada masa matsalar se cewa yayi wai ze iya sakanta taje ta aure wanda ze biya mata bukata
Kuma tanada yara tana tunanin tarbiyarsu in ta bar gidan
Ina jiye masa tsoran fadawa halaka ne malam.
AMSA
=====
👇
Malaman Duniya. Tin daga Kan Salaf har Kalaf suna Ganin Cewar, Idan Har mutum yana da ikon da zai Kara Aure. Abubuwan da zai Kalla kafin ya kara wannan Auren bai Tsaya Iya Kudin da yake da shi ko Abinda zai Iya ciyar da wannan Matar Kawai Ake kallo ba.
Wajibi ne ya zama yana da ikon ciyar da wannan matar da daukan sauran Dawainiyar ta na yau da Kullum. Tin daga Magani da Tufafi da Kare mata Mutuncinta da Kiyaye Surrunta da dai Sauransu. Wanda kowa ya sani Nauyi ne da ya Dorawa kansa. Sakamakon wannan Auren da yayi.
Wannan bai Tsaya Iya wadannan abubuwan Kawai ba. Dole ne sai yana da ingantacciyar Lafiyar Jiki da zai Iya gamsar da wannan matar da zai Aura d kuma matarsa da take Cikin Gidansa. Koda kuwa ita kadai ce. Bare kuma Mutumin da bashi da ingantacciyar Lafiyar da baya Iya gamsar da Matar da take Zaune a Karkashinsa ta Aure. ina Maganar dakko ya Auri Budurwa Mai Matsakaicin Shekaru, mai Bukatar Namiji, Mai Tashen Balaga. Wadda a Daidai wannan Lokacin ne take cikin Hadarin Rayuwa.
Idan har da Gaske ne, Mutumin da yake Cikin irin wannan Halin ne yake tunanin ya kara wani aure. To fa Maganar Gaskiya Akwai Matsala. Kuma ba makawa Abu guda Ukku ne zasu faru.
1. Ko dai ya zama wannan matar da zai Aura ta Zauna da shi a cikin Kunci da takura. A haka Abin zai dameta ya damu na Kusa da ita. Wadanda zata Iya Bude masa surrun damuwar ta. Idan ha Namiji ya san haka. To fa hakan ZALUNCI ne. Kuma Wallahi Akasarin Masu Irin Wannan Matsalar. A Lokacin da Wannan Matsalar ta bayyana, ba sa sakin mace da dadin Rai. Sabida na Sha cin Karo da irin Wannan Case din Yafi Sau Adadi.
2. Ko kuma ta zauna da shi tane Cin Amanar Sa. Ma'ana tana Samun Wasu Mazan Suna Biya Mata Bukata a waje. Kinga kenan idan har Wannan abin ya Tabbata, kenan ya yarda shi ya Zauna da gangan jikinta a gidansa, yana Kallon kyawunta, Wasu kuma suna yin Abinda suka Gadama da Ita a waje. Ma'ana wani chan yana wasan kura da ita. Wallahi an sha Samun Wannan Matsalar ba Adadi. Ko kuma.
3. Shi Mijin yasan baya Biya Mata Bukatarta ta 'ya mace. A haka Idan ya ga kamar ba ta damunsa Akan wannan Matsalar. Sai yana zarginta da Cewar tana Yin Zina. Ta ko Ina dadai Matsala Ce. Kuma Dukkan Abjnda Na Lissafo babu wanda baya Faruwa.
Sabida Haka Shawara ta Anan shine.
Wanda ya san ba zai Iya gamsar da mace Sama da daya ba. Ina Maganar kuma Karin Aure a gare shi.? Da zai Hakura Hakan Zaifi Zama Alkairi. Domin Gudun Matsalar da Hakan zai Harfar Masa.
Musamman Mutanen yanzu. Mazansu da matansu. Kashi 80 na Samarin wannan zamanin. suna da Karfin Sha'awa. Haka zalika kazo 99 na 'yan Matan wannan Zamanin suna da Karfin Sha'awa.
Kaga Kuwa bai dace ga wanda yake da deficiency ta wannan Bangaren. Musamman ma kuma ga wanda bashi da Lafiya akwai damuwa Kam.
Allah shine Masani.