SHAFA FUSKA BAYAN KAMMALA ADDU'A



SHAFA FUSKA BAYAN KAMMALA  ADDU'A

*TAMBAYA*❓

Malam menene hukuncin shafa hannu a fuska bayan gama addu'a.

*AMSA*👇

To dan'uwa hadisi ya zo daga Umar- Allah ya yarda da shi- cewa: "Annabi ï·º idan ya daga hannayansa ya yi addu'a ba ya mayar da su, har sai ya shafa su a fuskarsa"  Sunanu Attirmizi: 3386.

Wannan hadisin ya zo da hanyoyi masu yawa, saidai dukkansu suna da rauni, wannan yasa malaman hadisi suka yi sabani game da ingancin shi, Ibnu Hajara ya kyautata shi, saboda ya zo ta hanyoyi da yawa, kamar yadda ya bayyana haka a Bulugul-maraam a hadisi mai lamba ta: 1345.

Akwai wadanda suka raunana shi saboda suna ganin hanyoyin da yazo da su masu yawa, ba su kai su karfafe shi ya zama Hasan ba, wannan shi ne ra'ayin Ibnu Taimiyya kamar yadda ya bayyana haka a Majmu'ul fataawaa 22\509, haka Albani a Silsila Sahiha 2\146.

Malaman Fiqhu sun yi sabani game da shafar fuska bayan addu'a, wasu sun tafi akan mustabbancinsa, saboda sun gamsu da kyautatawar da Ibnu-hajar  ya yiwa hadisin, kamar Ibnu Bazz a daya daga cikin fatawoyinsa, akwai kuma wadanda suka tafi akan cewa ba za'a ayi ba, saboda rashin ingancin hadisan da suka zo akan haka.

Abin da na fahimta a wannan mas'alar shi ne ba za'a aibanta wanda ya shafa fuskarsa ba bayan addu'a, tunda yana da magabata .

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)