TSORATARWA AKAN WANDA BAYA YIN SALLAH.



TSORATARWA AKAN WANDA BAYA YIN SALLAH.

Sallah dayace daga cikin rukunnan musulinci guda biyar wanda musuluncin bawa baya cika har ya tsayar da ita.
@Muslim

Mazon Allah s.a.w yana cewa:
*(Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci,shine barin Sallah).*
@Muslim

¤Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Alqawalin da yake tsakanin mu da kafurai itace sallah, dukkan wanda ya bar sallah to ya kafirta).*
@ﺳﻨﻦ ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﻭﻏﻴﺮﻩ.

¤Imam Tirmizy ya ruwaito daga Abdillahi bn Shaqeeq al’uqaily yace:
*”Sahabban Annabi Muhammad s.a.w basu ganin barin aiki wani aiki kafircine inbanda sallah”.*
@ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ.
Wato sun hadu akan dukkan wanda yabar sallah kafirine.

¤Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Farkon abinda za’ayi wa bawa hijabi akansa na aiyukansa shine sallah,idan tacika tayi kyau ya tsira kuma ya rabauta,idan batayi kyauta kuma bata cika ba ya halaka ya tabe,idan an sami naqasa acikin farilla, sai Allah yace:kuyi dubi shin bawana ya sallolin nafila,sai ku cike gubin farillah da ita,sannan sauran aiyuka su kasance kamar haka).*
@ﺍﻟﺘّﺮﻣﺬﻱ ﺃﻳﻀﺎ ﻭﻏﻴﺮﻩ.

¤Annabi s.a.w yana cewa:
*(Farkon abinda za’a fara yiwa bawa hijabi akansa na aiyukansa ranar alqiyama itace Sallah,idan tayi kyau to sauran aiyukansa ma sunyi kyau,idan ta baci sauran aiyukansa ma sun baci).*
@ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﻄّﺒﺮﺍﻧﻲ.

¤Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Wanda ya kiyaye Sallah yana da haske da hujja da tsira a gobe alqiyama, wanda kuma bai kiyaye sallah ba,baya da haske da hujja da tsira,aranar alqiyama yana tare da Qaruna da Hamana da fir’auna,da Ubaiyu bn Khalaf).*
@ﻭﺭﻭﻯ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﻏﻴﺮﻩ.

HUKUNCIN WANDA BAYA SALLAH.

Wadanda basa yin sallah nau’i biyune:

1-Nafarko
*”Wanda ya bar yin sallah da gangam tare da kin yarda akan wajibcin sallah, wato bayayin sallah kuma yana ganin yin sallah ba wajibi bane,to wannan kafirine abisa haduwar dukkan musulmai baki daya, kuma kafircin da yake fitar da shi daga musulinci gaba daya”.*

¤ابن القيم رحمه الله:
Yana cewa:
*”Babu sabani a tsakanin malamai cewar wanda ya bar yin sallar farillah da gangam,yana cikin mafi girman zunubi kuma laifine daga cikin manyan laifuka wanda yafi laifin kisan kai da fashi da makami,yafi laifin zina da da shan giya da dukkan wani laifi, kuma sakamakonsa shine halaka da tabewa da masifa tun daga nan duniya har zuwa lahira”.*

2-Na biyu
*”Wanda bayayin Sallah saboda kasala da ha’ince wani lokacin yayi wani lokacin yakiyi,amma tare da yardar cewa yin sallar wajibine, wannan shine yana cikin laifi mai girma kuma yana cikin alamar munafinci babba,mai wannan halin za’ayi masa nasiha da wa’azi cikin hikima…..”.*

Malamai sun kasu kashi ukku akan mai wanann halin;-

i-Imam Malik da Shafi’i da Imam Ahmad awata riwaya daga wajansa,sun hadu akan cewa:
*”Mai wannan aikin ba kafiri bane amma yana cikin fasiqai za’a nemi ya tuba,idan ya tuba to idan kuma bai tubaba za’a kasheshi a matsayin Haddi da takobi”.*

ii-Wasu daga cikin magabata sun tafi kaman yana zaman kafiri,wannan itace dayar riwayar Imam Ahmad da wasu daga cikin malaman Shafi’yya.

iii-Amma Imam Abu Hanifa ya tafi akan wanda baya sallah dan kasala da ha’inci tare da yarda da wajibancin Allah,cewa:
*”Baya zaman kafiri kuma baza’a kashe shiba sai dai za’a matsa masa har sai yayi Sallar”.*

Allah ne mafi sani.

*Allah ka bamu ikon tabbatuwa akan yin sallah akan lokacinta kuma cikakkiya irinta Annabi s.a.w har zuwa mutuwarmu.*

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)