YADDA AKE NEMAN AURE A MUSULUNCI



YADDA AKE NEMAN AURE A MUSULUNCI.!!

Neman Aure a Musulunci, ya bambanta da yawancin abinda yake faruwa yanzu a Qasar Hausa.
Addinin musulunci ya tsara mana irin Matar ko Mijin da Zamu aura, da kuma Yadda Za'ayi wajen neman Auren.
Manzon ALLAH (saww) yace Mana "KA AURI MA'ABOCIYAR ADDINI...."
Sannan Kuma yace mana: "IDAN MUTUMIN DA KUKA YARDA DA (YADDA YAKE RIKON) ADDININSA YAZO MUKU YANA NEMAN 'YARKU DA AURE, TO KU AURAR MASA. IDAN BAKU YI HAKA BA, FITINA ZATA AFKU ADORON QASA DA KUMA 'BARNA MAI GIRMA"
Saboda haka kunga kenan Kyakyawar tarbiyyah ita ce abin dubawa awajen Saurayi ko budurwar da za'a aura. Ba wai kudi ko Nasaba ko Kyawun halitta ko Muqami ba.
Su ma wadannan din ana son su. Amma ba su bane abinda ake fara dubawa ba.
YADDA ZA KA YI:
***********
Idan kaga wata yarinya wacce kake so, To farkon abinda ya kamata kayi shine Kayi Kokarin neman Izinin Manyanta tun kafin ka fara tsayuwa da ita.
Zaka iya sanar da ita cewar KANA SONTA ta hanyar wani ABOKINKA ko kuma Qawarta. Amma ba zaka fara Karbar Lambar wayarta ko kuma zance da ita ba Kai tsaye, har sai da yardar Magabatanku.
Bayan ka samu yardar Manyanta, Sai kuma Ku tsara ma Kanku Lokacin HIRA da kuma wajen da Za'ayi hirar, Gwargwadon yadda addini ya tsara.
* HARAMUN NE KU KE'BANCE AWANI GURI daga kai sai ita (kamar yadda yawanci ake yi yanzu).
Koda kuwa baka jin komai azuciyarka..
Irin hakan shi yake sawa ake afkawa cikin zinace-zinace.
Manzon Rahama (saww) yace: "BAI HALATTA GA WANI MUTUM YA KEBANCE DA WATA MACE BA, SAI DAI IDAN SUNA TARE DA WANI MUHARRAMI".
Awani hadisin kuma, cewa yayi: "IDAN NAMIJI YA KEBANCE DA WATA MACE, (daga shi sai ita) TO SHAITAN SHINE NA UKUNSU".
* BAI HALATTA KU ZAUNA DAF-DA-JUNA BA.
* BAI HALATTA KU RIQA TA'BA JIKIN JUNA BA.... Ballantana rungumar juna, etc.
* Yafi kyau idan har yarinya ta samu manemi, to agaggauta aurar da ita.
Jinkirin da ake samu, shima yana sanya yawaitar zinace-zinace.
* Sannan kuma Za'a iya zama tsakanin iyalan saurayin dana budurwar su zauna atsakaninsu, su tsara yadda harkar auren zata gudana.
* zai fi kyau acire duk yawancin abubuwan da ake yi na Al'ada.. Atsaya akan abinda addini ya koyar.

(WALLAHU A'ALAM).

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)