ALHAJI DA DIREBA



ALHAJI DA DIREBA

Wani alhaji ne ya takurawa direban sa kullum fada ba kakkautawa, shi kuma direba kullum neman hanyar da zai rama yake.

Rannan sun fita unguwa a mota a cikin daji sai alhaji yace fitsari yake ji a tsaya. Direba ya tsaya alhaji ya fito yana fitsari, kawai sai direba ya sauko daga mota ya ruga a guje ta gefen alhaji, shi ma alhaji da gani direba sai yabi bayan shi suka yi ta gudu har alhaji ya gaji ya fara nishi, wayyo, wayyo, wayyo, suka tsaya. Sai alhaji yace direba me ya faru ne kake gudu? Sai direba yace ”alhaji wallahi excercise nake, ina motsa jiki na ne.
Post a Comment (0)