YADDA AKE YIN SALLAH A JIRGIN SAMA DA MOTAR HAYA



YADDA AKE YIN SALLAH A JIRGIN SAMA DA MOTAR HAYA

*TAMBAYA*❓

As alkm Gafarta Mallam ya halatta yin Sallar Farilla a cikin Mota/jirgin Sama da na Ruwa? domin wasu lokutan Mutum ya kan yi tafiya mai nisa zuwa jahohin kudu ga lokacin Sallah ya yi basa Tsayawa domin ayi Sallah, sbd mafi akasarin fasinjojin Ba Musulmai ba ne, kai har direban ma ba Musulmi bane. 

*AMSA*👇

To dan'uwa ya halatta ka yi sallah a jirgi ko mota, idan ya zama ba za ka sauka ba, sai bayan lokacinta ya fita, saboda fadin Allah madaukaki "Kuma Allah ya wajabtawa muminai sallah a cikin lokuta kayyadaddu" Surattunnisa'i aya ta:103. Amma mutukar zaka iya riskar lokacinta bayan ka sauka, to ka jinkita ta daga farkon lokacinta, shi ya fi, saboda ka samu damar cika ruku'u da sujjada yadda ya kamata, hakanan idan tana daga cikin sallolin da matafiyi zai iya hada ta da 'yar'uwarta, kamar azahar da la'asar, ko magriba da Isha, saboda za ka iya jinkirta ta farkon, ka yi ta hade da ta karshen. Duk sallar da ka ji tsoron fitar lokacinta za ka iya yinta a jirgi ko mota gwargwadon yadda ka samu iko, don haka ya halatta ka yi nuni da ruku'u ko sujjada lokacin da kake sallah a mota, idan kuma jirgi ne mutukar ka samu damar yi a tsaye ba za ka zauna ba, sannan ka yi kokari a duka wajan fuskantar alkibla, sai in ya ta'azzara. Annabi s.a.w. ya halatta yin sallah a jirgin ruwa kamar yadda Albani ya inganta hadisin a Sahihul-jami'i a hadisi mai lamba ta : 3777, wannan sai ya nuna halaccin yi a mota da jirgin sama, saboda dukkansu ababen hawa ne. 

Allah ne mafi sani Jamilu Zarewa

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)