ALQUR'ANI MAI GIRMA MAGANAN ALLAH 🌹
Imam ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yana cewa;
🌹 "Tsarki ya tabbata ga wanda yasa maganansa ta zama abun raya zukata, kuma waraka ga abunda ke cikin zuciya.
🌹 Hakika babu abunda yake mafi amfani ga zuciya sama da karatun Alqur'ani hade da tadabburinsa, domin Alqur'ani ya kunshi duk abubuwan dake kawo farin cikin, da kuma halayen masu aiki, da matsayin wanda suka san Allah.
🌹 Sannan Alqur'ani shike gadar da soyayya da shauki da kuma tsoro, kwadayi, tawakkali, yarda, godiya, hakuri, komawa zuwa ga Allah dama sauran abubuwan da suke zama rayuwa ga zuciya, da kuma cikarta.
🌹Sannan kuma Alqur'ani shike tsoratarwa daga duk munanan halaye wanda sune ke lalata zuciya da halakata".
مفتاح دار السعادة ١/١٨٧
#Zaurenfisabilillah
TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah
FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/