ANNABI DA SAHABBANSA // 76
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
Duk da dumbin asarar da musulmai suka yi karo da su na rashin wannan gwarzo na muslunci wato Hamza RA, ba su yi sake qarfinsu ya kubuce musu ba, su ke riqe da fagagen faman gaba daya in ba sansanin mushrikan ba, an fado wasu gwaraza wadan da sun taka rawar gani wajen kawar da ginshiqin kafurci a wannan lokacin, kamar dai Abubakar, Umar, Aliy, Zubair, Mus'ab, Talha bn Ubaidillah, Abdullahi bn Jahash, Sa'ad bn Mu'az, Sa'ad bn Ubada, Sa'ad bnr Rabee' da Anas bnn Nadeer da dai sauransu.
.
Daga cikin gwarazan da aka riqa ambatarsu har da Hanzala bn Abi Aamir, Abu-Aamir shi ne wanda aka hada makircin na biyu da shi gabanin fara yaqin, Hanzala sabon aure ne ma, yana angwancinsa da iyalinsa aka buga kuge, nan take ya miqe ya bar amaryar ya zaro takobi ya fito, aka yi ta fafatawa da shi har sai da ya kai ga babban kwamandansu wato Abu-Sufyan, saura qiris ya kai shi lahira, ba don Allah SW ya qudurta cewa Abu-Sufyan din zai zama babban sahabi, surukin Annabi SAW, kuma daya daga cikin wadan da suka ba da rayukansu don ba wa Annabi SAW kariya a yaqin Hunain ba.
.
Don Hanzala ya riga ya tukuikuya Abu-Sufyan RA zai kai shi lahira kenan sai Shaddaad bnl Aswad ya hango shi, nan take ya far masa da sara har dai ya kashe shi, babansa kuwa Abu-Amin yana can tare da Khalid bnl Waleed inda suka hado farmaki mai qarfin tsiya har sau uku, sai sun yunquro da qarfi yadda za su auka tsakiyar musulmai su raunana su, sai sojojin sama da ke kan dutse su yi musu ruwan kibau nan take su watsa su, sai ya zama adadin sojojin muslunci duk da qarancinsa shi ne dai yake da qarfin mamaya a ko'ina, kenan an ci nasara a kan mushrikai.
.
KUSKUREN DA AKA SAMU
Wannan shi ne yaqi na biyu babba da muslunci ya fuskanta, duk abin da bai faru a Badar ba, to in ya faru a Uhud ya zama na farko kenan daga shi za a dauki darasi, wannan tsari na raba rundanar muslunci zuwa gida uku, wato sojin sama, da na doki da sojin qasa ba a yi irinsa a yaqin Badar ba, kenan rashin fahimtar hikimar hakan zai iya sakawa a yi kuskure, a bayyane dai an riga an gama da kafurai, nasara ta tabbata a hannun musulmai.
.
Abin da ya rage kawai a kama fursunonin yaqi, a kashe na kashewa, a tattara ganima, wadan da suka sami damar tserewa kuma su sha da qafarsu, nasara dai ta dawo hannun musulmai, mutum 40 daga cikin 50 din da ke kan dutsen nan suka sauko, sai Ibn Jubair da wasu mutum 9 suka yi saura a sama, wannan kuskuren na mantawa da wancan umurni ya kusa ya mai da hannun agogo baya, sai dai da yake Shari'a gaba dayanta akan san ta ne a lokacin da wani abu ya faru da yawa in kuskure ya faru ne ake sanin hukunci.
.
Saukar da sojin sama suka yi, sai ya ba wa kwamandan hadingwiwa na Quraishawa dama, wato Khalid bnl Waleed yadda ya balle da sojojinsa ya kewaya ta bayan dutsen ya hudo wa Abdullahi bnl Jubair da sauran maharban guda 9 ya gama da su shi da muqarrabansa, Allahu Akbar, Khalid RA bai san zai dawo ya zama Saifullahi ba, wanda Allah SW zai bude qasashen kafurci da takobinsa, ai yana cin galaba a dutsen sai suka kwarma ihu, yadda sauran kafurawan da suka nemi tserewa suka fahimta suka juyo gaba daya.
.
Nan take wata mai qarfin hali a cikinsu wato Amrah bnt Alqama Alhaarithiyya ta yi maza ta daga tutarsu, nan fa mushrikan suka sami damar tatturuwa a wuri guda, yadda su ma suka yi wa musulmai qawanya, tanan inda suka taru, da ta bangaren Khalid, Annabi SAW kuma yana daga baya da wasu 'yan mutane da ba su wuce 9 ba (Muslim 2/107), yanzu yana zabi guda biyu: Kodai ya ja da baya shi da su su tsira da rayukansu, ko ya qwala kira don sahabbansa su ji muryarsa su taru a wuri guda.
.
Nan take Annabi SAW ya sayar da ransa ya qwala kira, wanda hakan ma zai sa kafurai su san inda yake, don ya fi kusa da su sama da musulmai da ke gabansu, mushrikai suna sane da cewar ko ba don gaba da muslunci wanda Annabi SAW shi ne zuciyar ba, a wannan yaqin dai muryarsa tuta ce, don haka suka yi kukan kura kansa, qoqarinsu kawai su kashe shi, masamman yadda mutum 9 ne kawai tare da shi, komai qarfinsu kuwa ba su iyawa da yawan mushrikan nan.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248