BA TA HANYAR AUREN SUNNAH AKA SAMENI BA



BA TA HANYAR AUREN SUNNAH AKA SAMENI BA
:
*TAMBAYA*❓
:
Malam nakasance ina da uba amma bata hanyar auren sunnah ya sameni ba. Da chan ban damu dashiba da duk abun da ya mallaka amma yanzo
sakomakon rasuwar mahaifiyata na kasance ciki bukatar taimako domin bani da wanda zai taimakamin. Ko na nemi taimako baya bani. To shine da na yanke shawarar
1.NA KAISHI KARA KOTU.
2.NA KASHEHI
3.NA BARSHI DA ALLAH.
Malam ina naman shawara, wai shinma ina da hakkin ya taimaka min?
Nagode malam.
:
*AMSA*👇
:
Kasancewar ba tahanyar aure ya sameka ba, (koda akwai kwararan hujjojin da suka tabbatar da cewar shine yayi cikinka) to ai tunda ba ta hanyar aure bane to baka da wani hakki akansa. Kar ka yarda ka dauki kowanne irin mataki
akansa. Domin kuma indai shari’ar musulunci za’ayi, baka da wata hujja akansa. Idan ka kuskura ma kayi yunkurin kasheshi, to zaka afka cikin wani babban laifin da zakayi nadamarsa mutukar kana raye. Sannan kuma ga fushin Allah atare dakai.
Shawara anan ita ce: Kayi hakuri ka dangana Ka nemi sana’a wacce zaka tallafi rayuwarka da ita. Ka dauki kanka amatsayin maraya gaba-da-baya. Ka nemi ilimin addini dana zamani. Insha
Allahu idan ka tara ilimi mai amfani, watarana zaka zama abun sha’awa. Ita kuma mahaifiyarka kaci gaba da yimata addu’a kana nema mata gafarar Allah akan laifukanta.

JAMA’A wannan fa kaÉ—an kenan daga cikin irin tasirin da zina takeyi wajen lalata rayuwar al’ummah. Don haka jama’a mu nisanci Zina da dangoginta. Mu kuma nisanci yin zaman auren da bai halatta ba.

Wallahu a’alam.

Muhammad Auwal Umar

Yaku Yan'uwa masu albarka Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana. Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)