NASIHA



NASIHA:

Mu sani bayin Allah! Baka da wani gata da sanyin idaniya sama da Allah. Baka da wani majiɓincin lamari sama da Allah. Baka da wani masoyi sama da Allah. Al'amuran duniya suna da girma da wahala idan ka saki Allah da Manzon sa. Mu kyautata mu bi Allah mu bi karantarwar masoyin sa Annabi (SAW) mu yi ihsani mu bauta masa (Allah) tamkar muna ganin sa, mu dage da nafilfili. Mu kyautata ma makusantan mu da duk wanda mu'amala ya haɗa mu dashi. Mu yi hakuri mu kau da kai mu dage da ambaton Allah da fifita Haƙƙin Allah akan na kowa mu guje ma ƙyashi da hassada da sauran cutukan zuciya mu guji zato. Da sannu Allah zai yarda damu ya yardar da mu cikin zukatan bayin sa.

Ina roƙon Allah Ta'ala ya yarda damu ya yi Rahama gare ni da gareku.

#Zaurenfisabilillah

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)