BAYA HALASTA KA ROKI ALLAH WANI MUTUM AYYANANNE A CIKIN ADDU'A HAR SAI KA HAƊA DA IDAN ALKHAIRI NE A GARE KA



BAYA HALASTA KA ROKI ALLAH WANI MUTUM AYYANANNE A CIKIN ADDU'A HAR SAI KA HAƊA DA IDAN ALKHAIRI NE A GARE KA

 *TAMBAYA*❓

Slm alaikum mlm ya azumi ya ibada? Mlm don ALLAH inaso amin bayani shin laifine a wajen ALLAH na roqeshi ya bani wane? matuqar na yarda da tarbiya da hali da addinini da dabi'unsa? ko kuwa bai kamata ba? saide dole na roqi mafi alkhairi kawai, na haqura da furta sunan wanda nakeso din?

*AMSA*👇

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Baya halatta ka roƙi Allah wani mutum aiyananne, ba tare da ka haɗa da sharaɗin, idan alkhairi ne gare ka, saboda dalilai kamar haka:

Mu mutane zahirin al'amari muka sani banda baɗinin su, ma'ana baka san zahiri da baɗinin shi ba, Allah ne ya san ciki da bai na al'amuran bawa da duk wani abu, shi yasa yace

(وَقُلِ ٱعۡمَلُوا۟ فَسَیَرَى ٱللَّهُ عَمَلَكُمۡ وَرَسُولُهُۥ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۖ وَسَتُرَدُّونَ إِلَىٰ عَـٰلِمِ ٱلۡغَیۡبِ وَٱلشَّهَـٰدَةِ فَیُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ)
[Surah At-Tawbah 105]

Allah ya san ababe mu, sani na haƙiƙa, mu mutane bamu sani ba. A nan baka san haƙiƙanin wannan mutum ba, Allah yace 

(... وَٱللَّهُ یَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ)
[Surah An-Nur 19]

Sau tari abin da kake zato alkhairi ne gare ka, sai ya zamo sharri ne, kuma sau da yawa a kan samu akasin haka. Ma'ana, wannan mutum na iya zama sharri gare ki ko da a zahiri mutumin kirki ne, nawa hakan ta faru? 

(كُتِبَ عَلَیۡكُمُ ٱلۡقِتَالُ وَهُوَ كُرۡهࣱ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰۤ أَن تَكۡرَهُوا۟ شَیۡـࣰٔا وَهُوَ خَیۡرࣱ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰۤ أَن تُحِبُّوا۟ شَیۡـࣰٔا وَهُوَ شَرࣱّ لَّكُمۡۚ... )
[Surah Al-Baqarah 216]

Kuma mu mutane farkon al'amari muka sani, bamu san ƙarshen al'amura ba, ma'ana mutumin nan zai canza ko ba zai canza ba, duba da hadisin Annabi da yace, ɗan Adam ba zai gushe yana aikin ƴan aljanna ba, har sai ya rage tsakanin sa da aljanna kamar zira'i sai littafi ko rubutu ya rigaye shi, sai ya aikata aikin ƴan wuta, ya shige ta, iyazhan billahi.

(ٱلَّذِینَ إِن مَّكَّنَّـٰهُمۡ فِی ٱلۡأَرۡضِ أَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُا۟ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَمَرُوا۟ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَنَهَوۡا۟ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۗ وَلِلَّهِ عَـٰقِبَةُ ٱلۡأُمُورِ)
[Surah Al-Hajj 41]

A cikin wannan addu'a, akwai nau'i na tazkiya, wato tsarkake bawa, alhali Allah ya ja hankalin mu daga barin haka sai dai kyautata zato da fata.

(... فَلَا تُزَكُّوۤا۟ أَنفُسَكُمۡۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰۤ)
[Surah An-Najm 32]

Sannan babu wani nassi da ya tabbatar da salahar sa, zato ne kawai, duba da abin da ya baiyana ne a zahiri. 

Don haka abin da ya fi dacewa a shar'ance, shine mutum ya bi abin da Annabi ya koyar sai ya zauna lafiya 

وخير الهدى، هدى النبي صلى الله عليه وسلم

Ma'ana mutum ya gwama roƙon sa da sharaɗin idan mutumen ko kuma abun da yake so, alkhairi ne ga addinin sa da duniyar sa da ƙarshen al'amarin sa, kamar yadda Annabi ya koyar mana

خيرا لي في ديني وعاشي وعاقبة أمري

Idan mutum yayi haka, ya dace, yayi daidai, ko ya samu, ko bai samu ba, insha Allahu zai samu natsuwa kuma zai sallama wa Allah, ya yarda cewa abin ko kuma mutumin da ya so, ba alkhairi bane a wajen sa, sai dai a wajen wani daban. Haka kuma al'amarin yake, abinda zai zamo sharri ga wani, sai ya zamo alkhairi ga wani daban.

Irin wannan addu'a tana halatta a yi ta ne kaɗai, idan nassi ne ya tabbatar da salahar sa, misali, ya halatta mu ce Allah ya haɗa mu da Abubakar da Umar radhiyallahu anhuma a mazauni ɗaya, gobe ƙiyamah ba tare da sa wani sharaɗi ba, saboda nassi ya tabbatar da cewa su yan aljanna ne. 

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Yaku Yan'uwa masu albarka Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana. ku kasance damu domin ilimintarwa, fadakarwa tare da tunatarwa.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)