RANAR DUK DA MALAMI YAYI FASHI BASHI DA ALBASHIN RANAR



RANAR DUK DA MALAMI YAYI FASHI BASHI DA ALBASHIN RANAR

 *TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum an wuni i lfy Allah Kara maka lafiya da ilimi Mai albarka ga tambaya ta kamar haka ina karantar da yara alqurani akoi Dan abinda nasa za'a dinga biya na a wata 

Shin idan sunyi tsallake basu zo ba a watan zan karbi kudin cifcifne ko zan rage musu kudin tunda sun tsallake???


 *AMSA*👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Idan su ɗaliban ne, suka yi tsallake, a nan ba laifin ka bane, ka zo ka jira su har lokacin tashi ko kuma zuwa lokacin da suka aiko da saƙon ba zasu zo ba, zaka ɗauki kudin ka cif if ne. 

Amma idan kuwa kai ne kayi tsallake toh dole ka cire kudin wannan lokaci ko lokutan ka mayar ma su, don baka cancanta da su ba.

Shawara ita ce, me zai hana ka koyar masu da alqur'ani kyauta, amma ka nemi wata hanyar samun kudin ta daban, ina ganin zai fi, duba da cewa koyar da alqur'ani ibada ce, sannan duk wanda ya amshi wani abu a kan wata ibadah toh baya da ladar ta a wurin Allah, kamar yadda ya zo a alqur'ani 

( مَنْ كَانَ يُرِيدُ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا وَزِينَتَهَا نُوَفِّ إِلَيْهِمْ أَعْمَالَهُمْ فِيهَا وَهُمْ فِيهَا لا يُبْخَسُونَ أُوْلَئِكَ الَّذِينَ لَيْسَ لَهُمْ فِي الآخِرَةِ إِلا النَّارُ وَحَبِطَ مَا صَنَعُوا فِيهَا وَبَاطِلٌ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ ) هود/ 15 ، 16 .

Duk da cewa ga hadisin Annabi sallallahu alaihi wa sallama yace

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم :
( إن أحق ما أخذتم عليه أجرا كتاب الله ) أخرجه البخاري ومسلم

Amma ina baka wannan shawara ne, idan bai zamo tilas ka karɓi ɗan abinda ake baka ba, kamar yadda ka sani, Allah yace

(وَمَنْ كَانَ غَنِيّاً فَلْيَسْتَعْفِفْ وَمَنْ كَانَ فَقِيراً فَلْيَأْكُلْ بِالْمَعْرُوفِ) .

Wallahu ta'aala a'lam

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana. ku kasance damu domin ilimintarwa, fadakarwa tare da tunatarwa.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)