DAGA TASKAR ALQUR'ANI...!!
( ﺃَﻓَﻤَﻦْ ﻳَﻤْﺸِﻲ ﻣُﻜِﺒﺎً ﻋَï» َï»° ï»َﺟْﻬِﻪ ....)
1. Wanda ya rungumi hanyar bata ya bar hasken qur'ani da sunnah kamar wanda yake tafiya ne a kife, fuskarsa a qasa qafarsa a sama. Ya za'a yi ya gane hanya ko ya isa zuwa waje mai amfani, ko ya tsira daga abun da zai cutar dashi!!?
2. Wanda yake qin gaskiya yana wulaqanta kan sa ne. Tun da ga shi yana kifar da mafi darajar waje a gabbansa (fuska).
3. Kamar yadda ba'a yi fuska don ayi tafiya da ita ba toh haka zuciya ma ba'a yi ta domin ta qunshi bata da munafunci ba. Sai dai wanda ya canza halittar Allah daga asalinta.
4. Duk in da aka samu tafiya toh za'a samu hanya. Hanyar kuma ko dai mai bullewa ko akasin hakan. Shin kana ganin mai tafiya a kife zai gano hanyar kuwa?
5. Wani lokaci a qur'ani akan buga misali akan abubuwa guda biyu ba domin suna da kaman-ceceniya ba ; a'a sai Don hasken mai kyau ya qara bayyana munin hanya maras kyau ya qara bayyana.
6. Akan hanyarka ta neman yardar Allah kar ka jira kowa; ko da kuwa kai kad'ai ne a gidan ku, kai kad'ai ne dangin ku, kai kad'ai unguwarku, kai kad'ai ne ofis din ku...kai kadai ne ..kai kadai ne...a duk in da kake.
Dr Jameel Muhammad Sadis Hapizahullah