HUKUNCIN BUƊE GROUPS



HUKUNCIN BUƊE GROUPS

*TAMBAYA*❓

Assalamualaikum Inasan zan bude wani group ne wanda zanke tura abubuwan da suka shafi addini tho ina san kadan za6amin sunan da kake ganin yadace kamar sunan da ya fara da Darul ko Kuma Nurul.

*AMSA*👇

WaAlaikumSalaam: Shi group Whatsapp ko Facebook ko wani social Media Kamar Wata Makaranta ce. Kuma Hanya ce ta Yada Alkairi ko Sharri. Sabida haka kenan. Dole ne ya zama yana da Tsari. Wanda ya dace da Abinda su Wadannan daliban Zasu Gamsu da shi. Ba wanda ya Shallake Tunaninsu da hankalinsu ba.
Sabida haka Ya Kamata idan har An yadda da cewar Wannan group din An bude shi ne sabida yada Alkairi. To fa Wajibi ya zama Akwai Doka. Kuma akwai Malman da aka Amince da su Ingantattun Malamai Masu Kiyaye Amana Ta Ilimi da zasuke sharing din Abinda Suka Rubuta Sahihi ba shaci-Fadi ba.
Sannan Wajibi ne Wannan group din ya zama Wadanda zasuke tura Sakuna, ya zama sun Tabbatar da Gaskiyar wannan Sakon Kafin Suyi tura Zuwa group. Ba Kawai Ake kawo Wa mutane Abinda hankalinsu ba zai dauka ba.
Sannan kuma sai an Kulle wannan group din, ya zama babu wanda yake da Ikon Tura Sakuna Sai admins ne zasuke yada Abinda ya Inganta a cikin Group.
Na tabbata idan har ka bar group a bude Kawo ma ya turo Abinda yayi Ra'ayi, Zaka ga Shirme da Hauragiya.
Wani Ma Blue Film zaike tura Muku, Wani yana tura drama da Shirme, wani kuma yake Daukar Hotunan kansa da kansa yana turawa mutane Cikin group, Wasu kuma Kawai Sun bude Shirar Audio kenan a Tsakanin Mata da Maza a cikin group. A haka ne kuma duk wanda ya shiga Group din da Niyyar Ya Karu zaiji group din ya isheshi. Sabida Shirme yayi yawa. Alhalin kuma wannan group din yana amsa sunan group ne na Addini.
Sabida haka kenan. Dole group ya zama yana da Tsari, ka gayyato Malamai ko daliban Ilimi da zasuke sharing din Abinda kowa zai karu da shi. Kuma Wajibi ne ka Bude Na Maza daban Na mata ma daban. 

WALLAHU A'ALAM

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)