HAKKOKIN MA'AURATA



HAKKOKIN MA'AURATA
:
https://chat.whatsapp.com/IZhc4HXjGXFDOuOmx3ceZA
:
TAMBAYA❓
:
Assalamu Alaikum,malam yaya aiki? Dan Allah malam Ayi mana Karin bayani game da hakkin miji akan matarsa da kuma hakkin Mata akan mijinta
:
AMSA👇
:
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

HAKKOKIN MACE AKAN MIJINTA.

1. Ya biya sadakin ta.

2. Ya rike ta amana cikin girma da arziki, da kyautatawa.

3.Kar ya cutar da ita kuma kar ya bari yana sane a cutar da ita ko ya buÉ—e wata hanyar da za'a cutar da ita ya zamo garkuwa gwargwado iko a gare ta.

4. kada ya jinkirta wani bukatan ta ko hakkin ta, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba yaji tsoron ALLAH.

5. Ya dunga wasa da dariya da ita a gabadaya rayuwar su na aure, kamar yadda Annabi muhammad (S.A.W) yake yida matan sa, hakan na sabunta soyayya madauwamiya a zuciyoyin su da rashin gajiya da juna da marmarin juna.

6. Yayi hira da ita kamar yadda Annabi (S.A.W) yake zama da matayen sa, suyi hira kuma ya saurare su.

7. Ya karantar da ita ilmi na addini kuma ya kara karfafa mata gwuiwa akai, ko ya kaita ingantacciyar makarantar sunnah ta samu ilmi ya dunga tunatar da ita hakkin ALLAH a kanta taji tsoron ALLAH, da kuma gyara mu'amulolin ta.

8. Ya dunga lura da Kuskuren ta yana mata gyara cikin so da qauna cikin rarrashi har ta gane, ya kuma dunga yabon ta in tayi abu daidai na kyautata wa idan da hali yayi mata kyauta ma akai iya karfin sa.

9. In tayi Kuskure da ya sabawa addini ya nuna mata tayi Kuskure, kuma ya taya ta da addu'a sa'annan yayi mata nasiha.

10. Kar ya zamo mai cutar da ita ta hanyar duka ko ya mari ta ko zagi.

11. Kar ya zamo mara sirri yana tona mata asiri ya zamo duk abunda sukayi a rayuwar auren su yaje yana fadawa mutane a waje, wannan haramun ne ba siffa ce ta miji na gari ba.

12. Yabi duk sare saren musulunci yadda musulunci ya nuna a kyautata wa mace ya kuma dunga sauke mata hakkin ta gwargwadon iko.

13. Ya zamo taimaka mata ko Yan'uwanta a duk Lokacin da take bukatar taimako gwargwadon iko, kuma ya rike ta amana.

14. Ya zamo mai girmama iyayen ta, ya kuma nuna mata kulawa.

15. Ya siya mata duk wani kaya mai kyau na sutura ko na gyaran jiki ko kwalliya wanda za ta dunga masa kwalliya a cikin gida.

16. Ya zamo Mai kishin ta, domin ma ai wajibi ne ya zamo miji yana kishin matarsa da nuna Soyayya a gare ta.

17. Ya zamo mai ciyar da ita halal, yafita ya nemo musu abunda zasu ci halal kuma ya tsare musu mutuncin su.

18. Idan yayi mata laifi ya zamo Mai neman ta gafarta masa.

19. Ya dunga sanya mata farin ciki, har ya zamo fara jin ba wanda ya fita dacen miji nagari.

20. Ya dunga tayar da ita suna wasu ayyukan ibada tare, inda sarari suci abinci tare suyi hira suyi dariya tamkar mata da miji tamkar saurayi da Budurwar sa tamkar yaya da qanwa su zama tamkar É—aliba da malamin ta.

21. Ya zamo Mai tausaya mata da nuna mata lallai ita macece kyakkyawa yar amana mai mutunci yar gidan mutunci mai cikakkiyar ni'ima kuma sarauniya abun girmama wa.

 HAKKOKIN MIJI AKAN MATARSA

1). HAKKIN BIYAYYA GA MIJI. Wananna shine hakki mafi girma akan mace, wajibine tabi umarnin sa ko bata so ta kaucewa halinsa ko tanaso aikata abunda ya hanata.
Wato yi nayi bari na Bari, amma fa biyayya tanada sharadi shine bazata bi Shiba, inya umurceta ta aikata abunda Allah ya hana.
Koya umurceta ta bar abunda Allah ya wajabta.
Sannan kuma ta kasance tanada ikon aikata abin da yayi mata umarnin.
Anan yakamata miji ya kasance mai tausasawa da hikima da bi sannu wajen bada umarni da hani.

2) Ta zauna a gida ta kula da gidan da tarbiyar ya'yanta, kada ki fita ko ina saida izinin mijinki.

3) Duk lokacin daya bukaceki ki amsa kiranshi, cikin sakin fuska, ki biya masa bukatarsa gwargwadon yanda zaki iya Saidai in baki da lafiya ko Bakida tsarki, to saiki bashi hakuri, cikin tausasa kalamai, tareda sanyayamai zuciya.
Kokuma in rashin tsarkine uzurinki to saiki sakarmai jikinki kuyi wasanni kala- kala har bukatarsa tabiya.
Ki kuma yimasa alkawarin farantamai, dayin shagali da zarar kin tsarkaka.
Dayawan mata sunayin kuskure, yayin da mijinta ya nemeta bata cikin tsarki, sukan bar mazan nasu cikin damuwa, da kewa har zuwa lokacin da zata tsarkaka.
Yake yar'uwata akwai hanyoyi da dama wa inda Zakiba wajen biyama mijinki bukatarsa batareda yashiga damuwaba, ko kin sanyashi cikin kewa rashin ki.
Akwai hanyoyi da dama wa inda zakibi wajen biyama mijinki bukatarsa...........

4) Kada ki yarda wani ya shiga gidansa saida izininsa, Koda kuwa yan'uwansa ne ko yan'uwanki.
Musamman cikin dakinsa ko kujerarsa, ko shinfidarsa.

5) kada kiyi azumin nafila yana gari saida izininsa.

6) Kada kiyi kyauta da kayansa saida izininsa, Amma Babu laifi ki baiwa bakinsa ko naki abunci, ko kibaiwa mabukaci amma batareda Kinyi almubazzaranci da mugunta ba.

7) ki kula da aikace-aikace gida da kula da yara, kamar tsaftace gida, girki akan lokaci, wanke wanke da shara, da hidimomin shi kanshi mijin.
Lallai ne yar'uwata ki hakuri tareda juriya wajen waÉ—annan hidimomin masu yawa da nauyi,
Kisani cewa ba aikin banza kike yiba, ibada ce babba.
Kai kuma miji karunga taimaka mata, a lokacin da kake gida karkace zaka barta da aiki ita É—aya, inka taimaka mata Zataji dadi Hakan na kara soyayya da shakuwa tsakanin ku.

8) Wajibi ne ki kare kanki Babu ruwanki da kowa, sai mijinki Koda kannan miji kada ki saki jiki dasu.
Ki tsare masa dukiyarsa, tareda tattala masa.
Ki kula da ya'yansa Koda kuwa bake kika haifesu ba, karki cutar dasu. Kisani inhar kika cutar dasu Allah zai musu sakaiya
kuma soyayyar ki zata ragu wajen mahaifinsu.

9) Ki kasance me godiya ga mijinki, mai yada alkhairin sa da yabonsa.
ki zama me boye sirrin mijinki da naki, kisani ciki badan tuwo kawai aka yi Shiba.
Kiyi zama da mijinki zaman amana da rufama juna asiri.

10) Yar'uwata ki kula da jikinki ki runga caba kwalliya irin wacce yake so.
Kirunga yi mishi shiga irinta garari, wadda zataja hankalinshi zuwa gareki.
Ki yawaita yi mishi murmushi da rausaya murya, tareda dadaÉ—an kalamai na soyayya.
A yayin da kike tare da mijinki Kirunga sarrafa jikinki tayanda zaki ja hankali shi zuwa gareki.
Ki dage ki cire kunya, kisani tsakanin miji da matarsa babu kunya.
Dan haka ki cire kunya ki tattali mijinki, kibashi kulawa.
Ki natsu a lokacin da kuke tare Kirunga aika mishi da wasu zafafan kalamai, tareda soyayya me rikitarwa, wadda zata matar dashi kawace mace a yayin da kuke tare.
Yar'uwata kisani basaikin bi boka ba, balle wani malamin tsubbu, dan ki mallaki mijinki, Ki runga kaima wani kato kudinki yana cin kaji, yaci Abun dadi, ki kasa zaman lafiya ,ke baki ciba wani kato yaci miki.
Yake yar'uwata, kisani kyautata da biyayya, da tattali da nuna soyayya, da kulawa, Da rukon Amana da gaskiya, sukadai sun isa idan kika ruke zaki mallaki mijinki.
Kidage ki koyi soyayya kala kala, ki natsu ki koyi dadaÉ—an kalamai.
Wanda su kadai idan kika ruke, zaki mallaki mijinki, batare kin kaima wani kato sisinki ba.
Ga banar kudinki, ka sabama Allah. wa iyazubillah. Allah ka tsaremu.

11)Kada kiyi mishi gori saboda wani ciko, da kika yi mishi ko wani nauyi da kike dauka.

12) Ki kasance me hakuri da abunda ya samu, da wadatar zuciya, kada ki dora masa abunda yafi karfinshi.

13) Kada ki aikata duk wani abu da kikasan zai bata masa rai, ko abunda zai cutar dashi.

14) Ki runga mutunta iyayen shi, da danginshi, da girmamasu da kyautata musu.

15) Duk abunda zai tabbatar da dorewar aurenki to kin runga aikatashi.
Ki guji cewa mijinki ya sake ki komai É“acin ran da kike ciki.
Saidai in akwai hujja ta shari'a.

16) Ki kasance me boye sirrin mijinki. kada ki kasance me tona asirin mijinki.
Musamman sirrin daya shafi kwanciya, da al'amurran rayuwa na Yau da kullum.

17) Ki kula da damuwar sa, da farin cikinsa. Wato kada ki aikata abunda zai bata masa rai.
Idan yana cikin damuwa kiyi kokarin faranta masa ai har sai kin tabbatar duk wananna damuwa ta yaye, tare da yi mishi Nasiha da tunatarwa.
.
Idan yana cikin farin ciki Karki kawo duk wani abu dakika san zai bata masa rai. ki kokarin kara masa farin ciki.
Yaa ke yar'uwata ki nuna damuwar ki ga mijinki a yayin da yake ciki damuwa fiyeda damuwar shi, Karki nuna rashin kulawarki, ko damuwa da damuwar da yake ciki.
Ki kokarin bin hanyoyin da zaki sashi farin ciki.
Ki nuna farin cikinki fiye danashi a lokacin da yake cikin farin ciki.

ALLAH yaba duk masu aure ikon sauke hakkokin da ke kansu. Ya zaunar dasu lafiya da masoyansu wato mazajensu.

Yaku Yan'uwa masu albarka Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana. Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH
Post a Comment (0)