YADDA AKE YIN WANKAN HAILA



YADDA AKE YIN WANKAN HAILA
:
TAMBAYA❓
:
Assalamu alaikum malam dan allah inaso  ayi min bayanin yadda ake wankan haila nagode.
:
AMSA👇
:
Wa'alaikumussalamu Warahmatullah.

Wankan haila, da na janaba da na biki da sauransu duk ɗaya ne, babu wani bambanci sai a Niyya.

Ga siffar Wankan janaba nan kamar yadda ya zo a hadisin Ummuna Aisha (r.a):

An karbo hadisi daga Aisha (r.a) ta ce: ((Manzon Allah (ﷺ) ya kasance idan zai yi wanka na janaba, yana farawa da wanke hannayensa, sannan sai ya zuba ruwa da damansa a bisa hagunsa, sai ya wanke farjinsa, sannan ya yi alwala. Sannan ya kama ruwa sai ya shigar da yatsunsa a cikin asalin gashin kanshi, sai ya zuba ruwa a kanshi sau uku, sai ya game jikinsa da ruwa, sannan ya wanke kafafunshi)). Bukhary da Muslim, lafazin Muslim ne.

A takaici wannan hadisin na koyarda mu yadda ake yin wankan tsarki ne, imma (janaba, haila, biki, Wankan Juma'a da sauransu).

'Yar uwa idan kin tashi za ki fara ne da wanke hannayenki, sannan ki yi tsarki da hannun hagu tare da wanke duk inda najasa ta ta6a, sannan sai ki yi alwala kamar yadda kika saba yi idan za ki yi sallah, sannan sai ki wanke gashin kanki tare da cuccudawa, ki sanya yatsunki har zuwa kasan gashin sau uku, sannan sai ki game jikinki da ruwa.

Babbar manufar dai shi ne ya kasance ruwa ya isa kowani lungu da sako na jiki, don haka duk inda aka ga ruwa be isa ba, sai a isar da shi.

Wallahu a'lamu.

✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.
 08166650256

Yaku Yan'uwa masu albarka Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)