```HARUFFAN ƘAUNA ¡¡```
*(Waƙar Gambara)*
```L...
Lemon zaƙi da jusi maƙil
Laƙaninsu duk ke ce ƙiril
Leda ke mai da su sabbi fil
Linzamin zaƙi ko a tafkin Nil
Luguden yawunki shi ne kuma fen'afil.
M...
Maganaɗisu a tsari da sifar koma
Majanyin zuciya ya haɗa da ni ma
Masaukin da ya aje ni ba dama
Musu ko tawili sai lambar girma
Me zai hana nai jinjinar bangirma.
N...
Nana ta ƙware a ɗaura zane
Na gan ta kan a ankara nai zane
Nuni na surar da ko kai wane
Ni'imar kallonta tabbas shi ne
Nau'in da zai sa tsuminka ya sane.
R...
Ranar bikinmu zan sha lakasera
Rauni ya ƙare dole ne na dara
Rumbin farinciki ai shi na tara
Rera waƙe kuma yanzu na fara
Rinton zunubi ahir rikici yai ƙaura.
S...
Satar zuciya tuni tai nisa
Sufi ya gan ta tun a nesa
Sassarfa ta yar da shi a ƙasa
Sauyi ya marabci rayuwarsa
Suɗar leɓe yake zuhudun an fasa.
T...
Tai kira zuciya ta amsa mata
Titiɓiri nake a makarantarta
Turare na humrar ƙaunarta
Tuni ya gauraye cikin zuciyata
Tes dubu na yi na ciwon sonta.
U...
Umarninki yau ya sa ni ruku'u
Ujila nake a so ban da shifa'u
Unguwarmu ana kira na Imru'u
Uban ƙauna Ƙaisu ya fi Yusha'u
Ungo zuciya kyauta ba taraju'u.
W...
Wiwin so na sha ina ta rawa
Wawar so nake cikin yunwa
Wainar zuciyarki har da ruwa
Wulla min a baki kar ki rowa
Wofantar da duk mai shewa.
Y...
Yayayyen maraya ya kurɓi giya
Yana tamɓelen ƙauna ba kunya
Yaya zai damu balle yai jinya
Yunwa da ƙishinki ai sun fi tsiya
Yo ai rashinki ne ke sa ni hajijiya.
Z...
Zallar so nake biɗa mai ziza
Zarya nai ta yi wurin yin biza
Za ni ƙasar da ba a yin izza
Zo ki raka ni sahiba kar ki gaza
Zuwanki fahari ne Ummu Aziza.
©ABOU OUTHAYMEEN
24-09-2021```