SHEKARA DAYA MIJINA BAI SADU DA NI BA, MENENE SHAWARA ??

SHEKARA DAYA MIJINA BAI SADU DA NI BA, MENENE SHAWARA ??


Tambaya
Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah yasamu dace. Malam don Allah ina son nasan matsayin aurena shekara daya mijina be kusanceniba alhalin muna tare kuma dukkanin mu muna lafiya. Nagode 

Amsa
Wa alaikum assalam,
 Auranku ingantacce ne,, amma zai yi kyau a kira magabatanku a tattauna matsalar, tun da saduwar ma'aurata ginshiki ne na Zamantakewar aure, wanda rashinsa yana kai ma'aurata zuwa saÉ“on Allah. In har ba ku cimma matsaya ba, bayan zama da magabata kina iya kai shi Kotu alkali ya muku hukunci, Saboda a musulunci bai Halatta miji ya kauracewa matarsa ba sama da wata (4) kamar yadda aya ta (226) a suratul Bakara ta tabbatar da haka.

Allah ne mafi sani 

08/06/2017 

Dr Jamilu Zarewa

https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Post a Comment (0)