MAGANIN INFECTION NA MAZA



MAGANIN INFECTION NA MAZA :

TAMBAYA TA 2309
***************
Amincin Allah su.tabbata ga Malam, Allah ya kara ma Nisan kwana da Ilimi mai amfani.
Don Allah don Girman Allah kataimakeni idan kanada iko akan wata matsala tawa kusan shekara biyu kenan akenema wallahi Mal. Yawan yin fitsari yana damuna kaman ace dasafe idan akwai sanyi zantayin fitsari amma idan akwai rana toh ba zanyi ba sosai. naje assibitoci dayawa kafin suka gane menene yake damuna suka min gwaje gwaje da dama suka ce min toilet infection mal. Shine matsalata Katemakeni damagani idan kana dashi

AMSA
***
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Akwai abubuwan da zaka iya yi da dama. Misali kamar :
Ka samu Furen Albabunaj, Ka rika zuba cokali uku da ganyen magarya cokali biyu. kana dafawa acikin ruwa kofi daya. Ka jefa tafarnuwa aciki ka dafa da ita.
Idan ya dahu sai ka taceshi ka sanya zuma aciki ka rika sha. In sha Allahu komai zai daidaita.
Allah ya sawwake.

WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)