HUKUNCIN LIMANCIN BEBE DA KURMA



HUKUNCIN LIMANCIN BEBE DA KURMA

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu


Malam menene hukuncin limancin BEBE (wanda baya
iya magana) DA KURMA(wanda bayaji amma yana iya magana)

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Limancin bebe wanda baya iya magana baya iya karanta Fatiha baya iya yin kabbarar Haramah bai ingantaba ya zama limami domin yafi mamun (masu binshi sallar) tawaya. Yazo acikin littafan fiqhu na mazhabobi guda hudu game da sharudan limanci: akwai nafarkonsu shine karatu tayinda anaso liman ya zama mai kyautata qira'ane sallah bata inganta sai da wannan.
sannan limancin kurma wanda bayaji shi ansamu sabani wasu malaman sunce yana inganta kurma yayi limancin sallah suna cewa hukuncin shi kamar hukuncin limancin makahone sunce ji da gani basu kebanta da wani sharadi daga sharuddan sallah ba (wato ba inda aka shardanta sai liman yana gani ko yana ji limancinshi zai inganta) Mazhabar malikiyyah suna ganin limantar da wanda ba kurma ba shine yafi kuma sunce makruhine (abin kyama ne) asa kurma wanda bayaji limami ratibi(na kullum-kullum) Hidabi acikin mawahibul jaleel yana cewa: Kai dalibin ilmi kasani shi kurma bai kamata ya asashi zama limami na kullum kullum ba saboda zai iya yin rafkanuwa (sahawu) ayi mai tasbihi baiji ba hakan kuma zai iya zama sanadiyyar bacin sallar kuma wannan itace magana mafi rinjaye

Wallahu A'alam.

_Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana._ 

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)