HUKUNCIN SANYA HOTON MAMACI A ‘SOCIAL MEDIA



HUKUNCIN SANYA HOTON MAMACI A ‘SOCIAL MEDIA

*TAMBAYA*❓

As Salamu Alaikum Wa Rahmatul Laahi Wa Barakatuh.
Da fatan malam yana lafiya.
Please, malam ya halatta a sa hoton mamaci a profile ko status?

*AMSA*👇

W alkm slm w rhmtul Laah w brktuh.
Abin da Malamai suka tabbatar a nan shi ne: Idan dai ba da larura (kamar na passport don shiga makarantu ko neman aiki ko fita ƙasashen waje da makamantansu) ba, musulmi ba ya yin harka ko mu’amala da hotuna na abubuwa masu rai (kamar mutum, dabba, tsuntsu, ƙwaro da sauransu), ko masu inuwa ne (kamar sassaƙaƙƙu ko ginannu), ko marasa inuwa (kamar waɗanda aka zana da hannu ko aka ɗauka da Camera). Saboda irin kausasa magana da tsawa mai tsanani da shari’a ta yi a kan haka:
[1] Abu ne sananne cewa: Hotuna su ne dalilin farko na kaucewar mutane daga kan hanyar Allaah tun a zamanin Annabi Nuhu (Alaihis Salaatu Was Salaam). Mutanen zamaninsa su ne suka sassaƙa hotunan manyan malamansu domin tunawa da su a farko, amma daga baya sai suka zama abubuwan bauta ba Allaah ba!
Daga ƙarshe kuma da aka turo Manzon Allaah Mai wa’azi na farko a duniya: Annabi Nuhu (Alaihis Salaam) domin ya hana su, sai kawai suka kangare kuma suka taurare, har ma suka riƙa faɗa wa mutanensu, kamar yadda Allaah Ta’aala ya ambato daga gare su:
ﻭَﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﻟَﺎ ﺗَﺬَﺭُﻥَّ ﺁﻟِﻬَﺘَﻜُﻢْ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﺬَﺭُﻥَّ ﻭَﺩًّﺍ ﻭَﻟَﺎ ﺳُﻮَﺍﻋًﺎ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﻐُﻮﺙَ ﻭَﻳَﻌُﻮﻕَ ﻭَﻧَﺴْﺮًﺍ
Kuma suka ce: Kar ku yarda ku rabu da Waddu da Suwaa’u da Yaguthu da Ya’uqu da Nasru.
A ƙarshe ƙissar dai hallaka ce ta same su, kamar yadda Allaah ya ce:
ﻣِﻤَّﺎ ﺧَﻄِﻴﺌَﺎﺗِﻬِﻢْ ﺃُﻏْﺮِﻗُﻮﺍ ﻓَﺄُﺩْﺧِﻠُﻮﺍ ﻧَﺎﺭًﺍ ﻓَﻠَﻢْ ﻳَﺠِﺪُﻭﺍ ﻟَﻬُﻢْ ﻣِﻦْ ﺩُﻭﻥِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺃَﻧْﺼَﺎﺭًﺍ
Saboda irin laifuffukansu sai aka nutsar da su a cikin ruwa kuma aka shigar da su cikin Wuta, kuma ba su samu wani mataimaki ba a bayan Allaah.
[2] Sannan a cikin Hadisai sahihai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi tsawa a kan al’amuran hotuna, kuma bai bambance ba a tsakanin nau’ukansu, kamar inda ya ce:
ﺃَﺷَﺪُّ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﻋَﺬَﺍﺑﺎً ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﻀَﺎﺣُﻮﻥَ ﺑِﺨَﻠْﻖِ ﺍﻟﻠﻪِ
Mafiya samun tsananin azaba daga cikin mutane su ne: Waɗanda suke kwaikwayon halittar Allaah
Haka kuma inda ya ce:
ﺃَﺷَﺪَّ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﻋَﺬَﺍﺏً ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻘِﻴَﺎﻣَﺔِ ﺍﻟْﻤُﺼَﻮِّﺭُﻭﻥَ، ﻳُﻘَﺎﻝُ ﻟَﻬُﻢْ ﺃَﺣْﻴًﻮﻥ ﻣَﺎ ﺧَﻠَﻘْﺘُﻢْ
Mafiya samun tsananin azaba daga cikin mutane a Ranar Ƙiyamah su ne: Masu yin hotuna, za a ce da su: Ku raya irin abubuwan da kuka halitta.
[3] Don haka, ba daidai ba ne musulmi ya riƙa amfani da hotunan mutane (rayayyu ko matattu, manya ko yara, kuma maza ko mata, haka ma sauran dabbobi ko tsuntsaye da sauransu) a cikin ‘social media’ kamar yadda aka bayyana a cikin tambayar, ko kuma a wani wurin da ba wannan ba, in dai ba da wata larura mai ƙarfi ba.
Maimakon haka sai ya yi amfani da hotunan abubuwan da ba masu rai ba, kamar itatuwa ko furanni ko duwatsu ko rana ko wata ko sararin sama ko rafuka ko teburori ko kujeru ko gidaje ko motocci ko jirage da sauran irinsu.

Wal Laahu A’lam.

*Shaikh Muhammad Abdullah Assalafiy*

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)