HUKUNCIN SANYA HOTON MACE A DP.



HUKUNCIN SANYA HOTON MACE A DP.

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum malam meye hukuncin mace tasa photon ta a dp matar aure ko budurwa? 

*AMSA*👇

Wa alaikumus salam.
Sanya hoton mace matar aure ko budurwa a social media haramun ne, ta sanya tufafi irin na musulunci ko a'a, domin mace fitina ce ga maza kamar yadda manzon Allah s.a.w ya fadi a hadisin usamah bin Zaid, inkuwa batayi shiga irinta musulunci ba to lefin yafi girma domin fitinar da zata haifarwa maza tafi tsanani, dan haka duk da sabanin malamai gameda hutunan na'ura shima namiji ya kiyaye dan fita daga sabani domin fita daga sabani mustahabbi ne. Mace ko ta yada hotonta a media haramun ne. 

Allah ne mafi sani

*Amsawa:*✍🏽 *ABDULLAHI ISMAIL AHMAD*

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)