HUKUNCIN WANDA SHAIDAN KE RIYA MASA SABON ALLAH AZUCIYARSA



HUKUNCIN WANDA SHAIDAN KE RIYA MASA SABON ALLAH AZUCIYARSA :
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum. Bayan Fatan Alkhairi Ga Malam.
Malam Ina Da Wata Babbar Matsala Wadda Na Tabbata Idan Na Bar Duniya A Wannan Lokaci Makomata Baza Tayi Kyau Ba! Wannan Matsalar Kuwa Itace : kullum Zuciyata Cike TaKe Da Wani Mugun Hali Na Aibata Allah Da Manzon Sa SAW (Wa'iyazu Billah).
Malam Wallahi Ba da Sona Take Hakan Ba Abin ne Kawai Yafi Karfina Kuma Na Rasa Yadda Zanyi, Malam Babu Sallah Daya Da Ke Wuce Ni. Gashi INA kokari Gurin yin azkar amma abun yaci tura. Malam kusan kullun sai nayi kuka idan na same kaina cikin wannan hali A Taimaka Min Da Mafita DoN Soyayyar Ka Da Annabi Muhammad SAW, Sannan Suma Daliban Wannan Zaure Mai Albarka Ina Bukatar Addu'ar su Don Girman Allah.
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Wannan matsalar irin taki, mutane da yawa sukan yi fama da ita. Amma tana samun asali ne daga shafar shaidanun aljanu. Su shaidanun ne suke shiga cikin zuciyar mutum suna sanya masa waswasi game da duk wani abu da ya shafi addini, Kuma suna tsirta masa miyagun kalamai game da Allah da Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Hanyoyin da zaki bi domin magance abun sun hada da:

👉 Kulawa da sallah, Azkar da kuma karatun Alqur'ani mai girma a kullum a ko yaushe. Ki rika yi kuma kina sanya audio da Qira'ah kina jinsa da earpiece.

👉 Kije ayi miki Ruqyah a waje amintacce mafi kusa dake. Ki tabbatar malamin ya fahimci matsalar, kuma yana da ilimin sanin "Ahwalul Jinn. Domin idan ba hakan ba, zai iya Qara jefaki cikin wani rudanin ne.

👉 Ki dena zama ke kadai. Kuma ki rika zama ko yaushe da alwala. Koda barci zakiyi ki tabbatar kinyi alwalarki kinyi addua'a sosai.

👉Ki rika yawan maimaita ayatul kursiyyi tare da zikirai masu Qarfi irin su La haula, HASBUNALLAHU, etc.

👉Ki rika yin a'uziyyah duk sanda tunanin yazo miki, tare da maimaita wannan addu'ar :
ﻫُﻮَ ﺍﻷَﻭَّﻝُ ﻭَﺍﻵﺧِﺮُ ﻭَﺍﻟﻈَّﺎﻫِﺮُ ﻭَﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻦُ ﻭَﻫُﻮَ ﺑِﻜُﻞِّ ﺷَﻲﺀٍ ﻋَﻠِﻴﻢٌ
(Huwal Awwalu wal akhiru waz Zahiru wal Batin, wa huwa bi kulli shay'in aleem).
ﺁﻣَﻨْـﺖُ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺭُﺳُـﻠِﻪِ .
Amantu billahi wa Rasulihi.

👉Ki dena kalle-Kallen fina-finai da karanta litattafai ko mujallu wadanda zasu iya janyo miki kallo ko saurarn abinda ya shafi sabon Allah.

👉Ki nemi Almujarrab na Zauren Fiqhu acikin tsirrai dake cikinsa akwai masu magance matslar waswasi.

👉Ki sani cewa Allah ba zai kama ki da wannan laifin ba, Mutukar dai baki furta akan harshenki ba, kuma baki aikata abinda suka riya miki ba. Akwai hadisin Manzon Allah (saww) dake cewa : "HAKIKA ALLAH YA GAFARTAWA AL'UMMATA ABINDA ZUCIYARSU TA ZANTAR DASU, MUTUKAR BASU FURTA BA".
Allah ya sawwake ya baki lafiya, ameen.

WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana.
Post a Comment (0)