HUKUNCIN YIN SALLAH DA TAKALMI?
:
*TAMBAYA*❓
:
ASSALAMU ALAIKUM MALAM KO YA HALATTA NAYI SALLAH DA TAKALMI?
:
*AMSA*👇
:
Babu Laifi Za'a Iya Yin Sallah Da Takalmi Matukar An Tabbatar Da Tsarkakarsa Ma'ana Babu Najasa Ajikinsa
* Dalili Kuwa Shine Alokacin Annabi S.A.W Sahabbansa Suna Sanya Huffi Suyi Sallah Dashi Akafafunsu
*Saidai Yana Da Kyau Acire Din Don Ladabi Da Girmama Ubangiji
Yana Halatta mutum yayi Sallah da takalma domin Manzon Allah {SAW} yayi kuma yayi Umurni da ayi.
Saidai kuma ba a koyaushe Annabi {SAW} ke yin Sallah dasuba.
danmi da ake Sallah da Takalmi? ana Sallah da takalma domin a Sabawa Yahudawa Annabi {SAW} yace : " kuyi Sallah da Takalma domin ku sabawa Yahudawa ". kada mu manta Sallah da takalmi Sunna ne.
FADAKARWA GA MA'ABUTA BIYAR SUNNAR FIYAYYEN HALITTA {SAW}
*Ya dan uwa kada ka manta Sallah da Takalma Sunna ne ba dole ba.
*Haka kuma ba'a Dauwama/Tabbata ana Sallah da takalma. yau kayi da gobe da jibi watarana kuma kayi bada Takalma ba {Wata rana kayi wata rana kayi bada takalmiba.
* Dan uwa kada kayi Sallah da takalma a duk inda zaka janyo tarzoma {idan ka sami jama'ar dake kula da masallaci basu aminta da ayi masu Sallah da takalma ba to kada kayi. ko idan takalminka zasu kazamta Masallaci duk dai kada kayi} idan kayi ka cutar da jama'a zaka iya samun ZUNUBI.
KANA IYA SALLAR FARILLA DA NAFILA DUK DA TAKALMA.
Allah ya daidai tamu akan hanya Madaidaiciya.
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana