HUKUNCIN YIN ALWALA A BANDAKI



HUKUNCIN YIN ALWALA A BANDAKI

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum warahamatullah. Malam tambayata ita ce: Mine ne hukuncin yin alwala a bandaki, kuma idan mutum ya gama zai yi addu'an da ake yi bayan an gama alwala a zuciya ne koko zai bari sai ya fito sannan ya yi ta?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salamu warahmatullah.

Yin alwala a banɗaki (bayi) ba laifi ba ne, musamman ma banɗaki na zamani da ake tsaftace shi a-kai-a-kai, amma idan da za a yi a wani wajen da ba banɗaki ba idan hakan ya samu da hakan zai fi, amma idan an yi a banɗakin ba laifi.
Game da addu'ar da ake yi bayan an gama alwala kuwa, bai kamata a furta ta a harshe a banɗaki ba, ya fi kamata a yi ta a zuciya, ko a bari sai an fito banɗakin sai a furta ta a baki, saboda makaruhi ne yin zikiri ko addu'a ko karatun Alqur'ani a banɗaki kamar yadda malamai suka tabbatar.
Sheikh IBN BAAZ ya ce: "Ambaton Allah a zuciya shar'antacce ne a kowane lokaci da kowane wuri, a banɗaki ko a waninsa: Abin da kawai aka qyamata shi ne ambaton Allah a banɗaki da harshe, saboda girmama Allah S.W.T. sai dai fa idan a farkon alwala ne za a iya faɗin kalmar "BISMILLAH" ( ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ) idan ba a sami damar yin alwalar a wajen banɗaki ba, domin faɗin Bismillah wajibi ne a wajen wasu malamai, amma sunnah ce mai qarfi a wajen mafi yawan malamai."
Duba Majmu’u Fataawa na Allama bn Baz (5/408).

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)