KABAR HAWAYENKA GA ALLAH.



KABAR HAWAYENKA GA ALLAH.
-
"A rayuwarka ka guji kai ƙarar Allah gurin bayinsa ƴan uwanka mutane, kaje kana bayyanar musu da damuwarka alhalin kuma ka bar wanda shi ne kaɗai zai iya magance maka abin da yake damunka a rayuwa"
-
"Haƙiƙa babban abin takaici ne za kaga mutum yaje gurin wasu jama'ar yana yi musu koken abin da yake damunsa, alhalin suma ɗin dukkanin su suna nema ne a gurin mai dika, wato Allah kenan"
-
"Sai mutum ya gama bayyanar da abin da yake damunsa ga mutane, ya gama faɗa musu sirrinsa, sai kuma su tila masa ƙasa a ido a maimakon su magance masa matsalarsa, amma shi kuwa Allah baya mayar da roƙon bawa a gareshi, sabida haka kada mu roƙi komai a gurin kowa face sai Allah shi kaɗai, domin shi ne yake da abin da zai bamu"
-
"Kada ka koka a gaban kowa babu makawa duk irin zafin raɗaɗin da kake ji a cikin zuciyarka, kabar hawayenka ga Allah shi kaɗai baza ka taɓa yin nadama ba, domin shi ne kaɗai zai iya magance maka dukkanin abin da yake damunka"
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
Facebook group
https://www.facebook.com/groups/4329860357034439/?ref=share
Post a Comment (0)