DUNIYA GONA CE TA LAHIRA.



DUNIYA GONA CE TA LAHIRA.
-
"Abin mamaki gareka, a lokacin da Allah buwayi ya nufeka da samun gona a wannan duniyar, kakan kyautata kula da shukar dake cikinta, amma ita kuma shukar ka ta lahira sai ka banzatar da ita ka wofuntar da ita, ko ka manta da cewa itama wannan duniyar gona ce a gareka ta lahira?"
-
"Lallai duniya itace kake neman lahirarka acikinta, sabida haka dole ne ka kyautata mu'amalarka acikinta domin ka girbi yabanya mai kyau a ranar ƙiyamah"
-
"Ita duniya tamkar gona take ga mutane, misalinta kamar misalin manomi ne, yadda idan damina tazo zai je ya shuka iri a gonarsa domin ya fitar masa da tsirrai da yabanya mai kyau idan lokaci yayi sai ya girbi kayansa, to haka shima bawa nagari yake shuka alkhairi acikin wannan duniyar ta yadda zai girbi abinsa a ranar lahira, wanda bai yi shuka ba baya girbar komai a gonarsa, to haka nan shima wanda bai aikata alkhairi ba, babu abinda zai girba a ranar lahira saidai nadama"
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
Post a Comment (0)