KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 05
.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa
.
NAU'O'IN SADARWA A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI
Masana a ilimin fannin zamantakewa sun faɗaɗa nau'ukan saƙo da ɗan'adam ke sadarwa ko ake sadar masa waɗanda suka haɗa da:
1. Saƙon da Ubangiji mahalicci ke sadarwa zuwa ga bayinsa ta hanyar aiko mala'ika zuwa ga zaɓaɓɓun manzanni.
.
ولقد بعثنا في كل أمة رسولا أن اعبدوالله واجتنبوا الطاغوت فمنهم من هدى الله ومنهم من حقت عليه الضلالة فسيروا في الأرض فانظروا كيف كان عاقبة المكذبين. (سورة النحل، آية ٣٦).
"Haƙiƙa mun aiko manzo ga kowace al'umma a kan ku bauta wa Allah, ku nisanci ɗagutu, daga cikinsu akwai wanda Allah ya shiryar, daga cikinsu kuma akwai wanda ɓata ya tabbatu a kansa, ku yi tafiya a bayan ƙasa, ku duba yadda ƙarshen masu ƙaryatawa ya kasance".
.
2. Saƙon da ɗan'adam ke sadarwa a tsakanin gaɓoɓinsa, kamar wurin da zuciya ko ƙwaƙwalwa za ta sadar da saƙo zuwa hannaye, kunnuwa ko idanuwan ɗan'adam.
3. Saƙon da mutane ke sadarwa ga junansu a dukkan fannonin rayuwar ɗan'adam wajen zamantakewa, mu'amala da sauransu. Wannan kuwa ya ƙunshi saƙo tsakanin mutum da mutum ko zuwa ga wasu keɓaɓɓun jama'a ko kuma ga al'umma baki ɗaya.
.
Don haka, sadarwa wani ginshiƙi ne a cikin mu'amalolin ɗan'adam wadda rayuwa ba za ta cika ba sai da shi. Amma abin da ya kasance kan gaba cikin waɗannan nau'uka na sadarwa shi ne wadda ya gina dangantaka tsakanin bawa da mahaliccinsa. Wannan nau'i ya sami tushensa ne tun daga mala'iku, Annabi Adamu (A.S), ya kuma ci gaba da gangarawa ta hannun manzannin Allah har zuwa wannan zamani da duniya ke ƙarƙashin saƙon manzancin Annabi Muhammad (S.A.W).
.
Wannan nau'i na sadarwa, musamman wadda ya game wannan al'umma tamu (watau al'ummar Manzon ƙarshe), shi ne wadda ya ƙunshi isar da saƙon Ubangiji (S.W.A) ga ɗaukakin bil'adama. An gina ginshiƙin wannan fannin saƙo ne ƙarƙashin kafofi masu yawa, waɗanda suka haɗa da:
i. Saukar da wahayi ga Manzon Allah (S.A.W) ta bakin mala'ika Jibril (A.S), na saƙonnin da ke ɗauke cikin Alƙur'ani da hadisin ƙudsi.
.
Wannan babbar kafar sadarwa ce tsakanin Allah (S.A.W) da bayinsa wadda Ubangiji maɗaukaki ya zaɓa kuma ya tsare tare da ba su kariya.
وما أرسلناك إلا كافة للناس بشيرا ونذيرا ولكن أكثر الناس لا يعلمون (٢٨).
.
ii. Hadisan Manzon Allah (S.A.W) sun kasance sadarwa ne tsakanin Ubangijin halittu da bayinsa ta bakin baɗaɗinsa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S.A.W), domim Allah (S.W.T) ya tabbatar mana da cewa Annabi (S.A.W) ba ya faɗin son ransa, duk abin da ya faɗi Shari'a ce da aka umurce shi ya isar. A cikin Alƙur'ani Allah (S.W.T) yana cewa:
وما ينطق عن الهوى (٣) إن هو إلا وحي يوحى.
"Kuma ba ya yin magana daga son zuciyarsa. (Maganarsa) ba ta zamo ba face wahayi ne da ake aikowa". Suratun Najmi, aya ta 3-4.
.
iii. Huɗubobin jama'a da na ranakun idi da sauran hanyoyin tabligi duk kafofi ne na sadarwa da isar da saƙonnin Allah (S.W.T) zuwa ga bayinsa.
ولتكن منكم أمة يدعون إلى الخير ويأمرون بالمعروف وينهون عن المنكر وأولئك هم المفلحون.
"Lalle ya kasance daga cikinku a sami wata al'umma da za ta riƙa yin kira zuwa ga alheri suna yin umurni da kyakkyawa, suna kuma yin hani ga mummuna, waɗannan su ne masu samun babban rabo. Suratu Ali'imrana, aya ta 104.
.
iv. Ginshiƙin musulunci guda biyar, watau furta kalmar shahada, salla, azumi da aikin hajji duk sun ƙunshi nau'uka na sadarwa da ƙulla mu'amala tsakanin al'umma musulmi.
Damar da musulmi yake samu don sadarwa tsakanin juna a yau da kullum ta waɗannan kafofi, babu kamarsu a dukkan nau'in zamantakewa da aka shimfiɗa a doron ƙasa.
.
Baya ga sadarwa daga Ubangiji zuwa ga bayinsa, har ila yau kuma akwai nau'ukan sadarwa wadda Allah (S.W.T) ya keɓance tsakanin jinsin wasu zaɓaɓɓun halittunsa, wadda kuma suka haɗa halittunsa ta ɗan'adam. Domin Allah (S.W.A) ya bambanta halittar ɗan'adam da ta sauran halittunsa ta hanyar keɓe jinsin mutane da hankali, tunani, fahimta, magana da tsararriyar mu'amala a tsakanin juna.
.
A bisa wannan bigire ne aka gina hanyoyin mu'amala na sadarwa da isar da saƙo a tsakanin jinsin ɗan'adam. Waɗannan hanyoyi kuwa sun tattara dukkan nau'ukan na rubutattun saƙonni, maganar baki, ishara da kuma zayyane-zayyane da mutane ke amfani da su wajen fahimtar da juna da musayen ilmi a tsakanin al'umma.
.
Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248