KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 03
.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Ganawa
.
TA'ALIƘI (II)
Dukkan yabo tsarkaka su tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad, ɗan Abdullahi, ɗan Abdulmuttalib; wanda Allah ya turo shi a matsayin rahama ga bayi. Ya Allah ka yi daɗin tsira gare shi, da iyalan gidansa tsarkaka, da sahabbansa, da duk waɗanda suka bibiyi bayansu da kyautatawa har zuwa ranar tsayuwa gaban Allah Maɗaukakin Sarki.
.
Abu ne sananne ga duk wanda ya bai wa shekaru 50 baya a wannan duniya a yau, cewa lallai halin da duniya take ciki a yanzu a fannin sadarwa, abu ne mai cike da ban mamaki irin wanda a sadda yake ƙarami, ko kaɗan bai taɓa tunani ko mafarkin wani abu makamancin haka ba. Tabbas komai yana da sababi. Babban sababi wajen samuwar wannan yanayi kuwa shi ne samuwar fasahar Intanet.
.
Fasahar Intanet, wanda tsari ne da ya ƙunshi aiwatar da sadarwa tsakanin na'urorin sadarwa - irin su Kwamfuta, da Wayar Salula dsr - tana ɗauke da wasu siffofi manya guda uku. Waɗannan siffofi kuwa su ne suka haɗu wajen samar da duk wani abin al'ajabi da ake gani a fannin sadarwa a yau. Siffa ta farko ita ce: "Game duniya".
.
Duk inda kake a duniya, ta hanyar Intanet, kana iya aiwatar da sadarwa. Babu inda wannan fasaha ba ta iya kutsawa. Sannan fasahar Intanet "Jakar magori" ce; duk abin da kake nema - a É“angaren ilimi - za ka samu a ciki. Sannan duk tsofaffin kafofin sadarwa - irin su rediyo, da talabijin, da jaridu, da fax - duk fasahar Intanet ta hukume su; idan ka shiga za ka same su.
.
Sai siffa ta uku, wato "Samar da ƙirkire-ƙirƙire". Yaɗuwa da bunƙasar wannan fasaha sun samu ne sanadiyyar ƙirƙire-ƙirƙiren da ita kanta fasahar ta sabbba samuwarsu. Duk sababin abubuwan da ke bayyana a wannan kafa na mamaki da al'ajabi, ƙirƙire-ƙirƙire ne ya samar da su. Wannan bunƙasa ya samar da wasu kafafen sadarwa na zumunci, waɗanda ke ɗauke da amfani, a ɗaya ɓangaren kuma suka haifar da illoli masu yawa a cikin al'umma.
.
Wannan littafi mai take: "KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI", wanda babban Malami SHEIKH ALIYU SA'ID GAMAWA ya rubuta mana, ya zo ne don magance waɗannan illoli da ke addabar mu musamman ma matasansu da galibin lokutansu na ƙarewa ne a kafafe na sada zumunta, wato: "Social" ke nan. Malamin ya dubu mahangar tarihi ne da kuna addini.
.
A ɓangaren tarihi ya dubi samuwa da bunƙasar wannan fasaha a taƙaice, da irin amfani ko illolin da suke ɗauke da su. A mahangar addini kuma ya faɗakar da mai karatu kan tasirin waɗannan illoli. Sannan ya bayyana ƙa'idojin da addini ya gindaya - ta amfani da mahangar Shari'a na samar da maslaha ga al'umma - wajen aiwatar da sadarwa kowane iri ne. Bayan wanann shimfiɗa mai muhimmanci, sai Malam ya dira kan hanyoyin kariya, duk a mahangar muslunci. A ƙarshen littafin marubucin ya kawo mana samfurin rubuce-rubuce da ya yi mana a wasu shafukansa da ke wannan dandali, don nuna mana a aikace "Ga yadda ya kamata abin ya kasance".
.
Saura da me? Ya rage ga kunne mai jin bari, ta ji bari. Ina roƙon Allah ya saka wa Malam kan wannan gagarumin aiki da ya yi. Haƙika Allah ya hore wa Malam juriya wajen rubutu. A iya sanina, wannan ɗaya ne daga cikin gomman littatattafan da ya rubuta, duk don faɗakar da al'umma. Allah ya amfanar da mu ba ki ɗaya, amin. Wassalamu alaikum.
.
Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik)
Garki - Abuja
08034592444
Imel: salihubdu@gmail.com
www.facebook.com/babansadik
Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248