KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 04
.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa
.
MA'ANAR SADARWA DA NAU'UKANSU
Sadarwa hanya ce da bil'adama ke ɗaukan nau'o'in saƙo ta kafofi mabambanta, don isar wa ga wani mutum ko gungun mutane ko ga ɗaukacin al'umma baki ɗaya. Har ila yau, ana iya bayyana sadarwa da cewa hanya ce ta fahimtar da juna a tsakanin mutane, a inda mutum zai karɓi wani saƙo daga wasu kafofi sannan kuma shi ma ya isar, ta hanyar cuɗanya da juna. A taƙaice dai, sadarwa na nufin isar da wani bayani, yaɗa wata fahimta ko manufa ko basira daga wani zuwa wani ta hanyar amfani da harshe, rubutu, alamomi ko hutana, ko wani nau'i na zayyane-zayyane.
.
Sadarwa ko isar da saƙo wani abu ne mai tushe da asali a mahangar addinin musulunci. An fara sadarwa zuwa ga halittar ɗan'adam tun kafin a samar da shi a gangan jiki, domin Allah (S.W.A) ya ba mu labarin tayin amana da ya yi wa halittunsa tun kafin samuwar ɗan'adam, sauran halittu suka ƙi, amma mutum ya amaa.
إنا عرضنا الأمنة على السموت والأرض والجبال فأبين أن يحملنها وأشفقن منها وحملها الإنسان إنه كان ظلوما جهولا.
.
"Lalle mu Mun gitta amana ga sammai da ƙasa da duwatsu, sai suka ƙi ɗaukar ta kuma suka ji tsoro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shi (mutum) ya kasance mai yawan zalumci, mai yawan jahilci".
Suratul Ahzab, aya ta 72.
.
Bayan wannan kuma, sadarwa ta farko ta tarihin ɗan'adam ita ce wadda ta kasance tsakanin Allah (S.W.A) da Mala'iku, yayin da Allah (S.W.A) yake bai wa Mala'iku sanarwar halittar Khalifancinsa a bayan ƙasa, wato samuwar halittar farko a duniya, Annabi Adam (A.S), Allah ya ce:
.
وإذ قال ربك للملائكة إني جاعل في اللأرض خليفة قالوا أتجعل فيها من يفسد فيها ويسفك الدماء ونحن نسبح بحمدك ونقدس لك قال إني أعلم ما لا تعلمندون.
"Kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce ga mala'iku: 'Lalle ne, Ni mai sanya wani halifa a cikin ƙasa', suka ce: 'Ashe, za ka sanya a cikinta wanda zai yi ɓarna a cikinta, kuma ya zubar da jinanai, alhali kuwa mu muna yi maka tasbihi game da gode maka, kuma muna tsarkakewa gare ka', Ya ce: Ni, na san abin da ba ku sani ba". Suratul Baƙara, aya ta 30.
.
Bayan nan sai sadarwar saƙo ga Annabi Adamu (A.S) a cikin Suratul Baƙara, Allah (S.W.A) ya ce:
وعلم آدم الأسماء كلها ثم عرضهم على الملائكة فقال أنبئوني بأسماء هؤلاء إن كنتم صادقين. قالوا سبحانك لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم. قال يا آدم أنبئهم بأسمائهم فلما أنبئهم بأسمائهم قال ألم أقل لكم إني أعلم غيب السماوات والأرض وأعلم ما تبدون وما كنتم تكتمون.
.
"Kuma Ya sanar da Adam sunaye dukkansu, sa'an nan kuma ya gitta su a kan mala'iku, Ya ce: 'Ku gaya mini sunayen waɗannan idan kun kasance masu gaskiya'. Suka ce 'tsarki ya tabbata a gare ka! Babu sani a gare mu face abin da ka sanar da mu. Lalle ne kai, kai ne masani, mai hikima. Ya Adam! Ka gaya musu sunayensu. To, a lokacin da ya gaya musu sunayensu, (Sai Allah ) Ya ce: Ashe ban ce muku ba, lalle ni ina sane da gaibin sammai da ƙasa, kuma (ina sane da) abin da kuke bayyanawa da abin da kuka kasance kuna ɓoyewa?". Suratul Baƙara, aya ta 31-34.
.
Haka kuma ya ƙara da cewa:
وقلنا يا آدم اسكن أنت وزوجك الجنة وكلامنها رغدا حيث شئتما ولا تقربا هذه الشجرة فتكونامن الظالمين.
"Kuma muka ce: Ya Adam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna, kuma ku ci daga gare ta, bisa wadata, inda kuke so, kuma kada ku kusanci wannan itaciya, har ku kasance daga azzalumai". Suratul Baƙara, aya ta 35.
.
Kamar yadda wadannan ayoyi suka nuna, Allah (S.W.A) ya fara isar da saƙo ga mutum ne ta hanyar tsakaninsa da mala'iku, sai ga shi Annabi Adam (A.S), a lokacin da yake gidan aljanna. Wannan kuma shi ne farkon sadarwa ga jinsin ɗan'adam baki ɗaya.
Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248