KYAUTATA WA IYAYE A BAYAN AURE



KYAUTATA WA IYAYE A BAYAN AURE

https://chat.whatsapp.com/LRPQDrs7qSoKXuSspoPkFm

*TAMBAYA*❓

_As-Salamu Alaikum_ ,
Na karanta littafinka: *Iyaye ko Miji?* Ya yi kyau ƙwarai, Allaah ya saka da alkhairi.
Amma ina da tambaya guda ɗaya:
Ana nufin a bayan aure iyayen mace ba su da sauran haƙƙi a kanta kenan?

*AMSA*👇

_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah_ .
[1] Da farko ya kamata mai tambaya ya san cewa: Dalilin rubuta littafin *Iyaye ko Miji* shi ne: Warware wata matsala da ta daɗe tana ci wa matan aure musulmi a yankinmu tuwo-a- ƙwarya, wadda kuma aka sha raba aure saboda rashin sanin gamsasshiyar amsa a kan ta, ita ce: Wanene ya fi cancantar mace ta yi masa biyayya a lokacin da aka samu saɓani a tsakanin iyayenta da mijinta?
Ko kuma a ce: Wanene a tsakanin iyaye ko miji ya fi girman haƙƙi a kan mace?
Wannan matsalar ce ɗan ƙaramin littafin ya yi ƙoƙarin warwarewa. Shiyasa ma a ƙarshensa aka ce:
‘Amma idan miji ya hana matar aikata wani abin da Allaah ya yi umurni, ko kuma ya yi mata umurni da aikata wani abin da Allaah ya hana, bai halatta gare ta ta yi masa biyayya ba a cikin haka, domin Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce: *‘Babu biyayya ga wani mahaluki a cikin saɓon Mahalicci.’*
Wannan ya nuna ba a cikin komai ne mace take yi wa mijinta biyayya ba.
[2] Amma maganar haƙƙoƙin iyaye a kan mace, wannan bai sauka daga kanta ba saboda ta yi aure. Har yanzu wajibi ne ta girmama iyayenta, ta mutunta su, ta gaya musu magana ta darajawa da martabawa, kamar yadda haka ya ke a kan mijinta shi ma dangane da iyayensa. Allaah Ta’aala ya ce:
*Kuma Ubangijinka ya hukunta cewa: Kar ku yi bauta ga kowa sai dai gare shi, kuma iyaye biyu ku kai matuƙa wurin kyautata musu. Idan ɗayansu ku dukkansu biyu ya tsufa a tare da kai, to kar kace musu tir! Ko kash! Ko Haba! Kuma kar ka tsawace su ko ka kaurara ko ka munana musu magana, amma dai ka faɗa musu magana ta mutuntawa da darajawa. Kuma ka tattara su gare ka, kuma ka ƙasƙantar da kai gare su saboda tausayawa. Kuma ka riƙa cewa: Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka rene ni a lokacin ina ƙarami* . _(Surah Al-Israa’i: 23-24)_
A wurin fassara maganarsa: *{Kuma ka tattara su gare ka, kuma ka ƙasƙantar da kai gare su saboda tausayawa},* Urwatu Bn Az-Zubair ya ce:
ﻟَﺎ ﺗَﻤْﺘَﻨِﻊْ ﻣِﻦْ ﺷَﻲْﺀٍ ﺃَﺣَﺒَّﺎﻩُ
Kar ka ƙi yin duk wani abin da suke so. _(At-Tabariy da Ibn Abi-Shaibah; Sahihi ne, in ji mai Rasshul Bard, shafi: 18_ )
Wannan ya nuna:
Kyautata wa iyaye abu ne da Allaah Ta’aala ya hukunta shi.
Allaah ya hana a yi wa iyaye duk abin da ke nuna ƙosawa ko gajiya da su.
Wajibi ne a gaya wa iyaye magana ta girmamawa da darajawa da martabawa.
Wajibi ne a riƙa tausaya wa iyaye, a nisanci duk abin da ba su so, in dai ba saɓo ba ne.
Wajibi ne a riƙa yi wa iyaye addu’ar Allaah ya rahamshe su.
A wata ayar kuma ya ce:
*Kuma mun yi wasiyya ga mutum dangane da iyayensa biyu - mahaifiyarsa ta ɗauki cikinsa rauni a kan rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu - cewa: Ka gode mini, kuma da iyayenka, makoma a gare ni ta ke. Kuma idan suka yi ƙoƙari a kan sai ka yi tarayya da ni a cikin abin da ba ka da iliminsa, to kar ka yi musu biyayya. Amma ka zauna tare da su a duniya cikin kyautatawa, kuma ka bi hanyar wannan da ya mayar da al’amura gare ni, sannan makomarku duk zuwa gare ni ta ke, sai in ba ku labari a kan duk abin da kuka kasance kuna aikatawa.* _(Surah Luqman: 14-15)_
Wannan ya nuna:
Mutum ya riƙa tuna asalinsa da yadda iyayensa, musamman mahaifiyarsa, suka wahala da shi.
Mahaifiyarsa ta ɗauki cikinsa tsawon watanni tara, kuma ta rene shi na tsawon shekaru biyu.
Dole mutum ya riƙa gode wa iyayensa a bayan godiyarsa ga Ubangiji _Subhaanahu Wa Ta’aala_ .
Haram ne musulmi ya bi iyayensa a cikin saɓon Allaah, kamar ta aikata manya ko ƙananan zunubai.
Dole ne musulmi ya kyautata wa iyaye ko da kuwa masu saɓo ne, ko ma in ba musulmi ba ne.
[3] Sannan a cikin Littafin *Al-Adabul Mufrad* , Mawallafinsa Al-Imaam Al-Bukhaariy ya fara shi ne da riwaito hadisai a kan wajibcin kyautatawa ga iyaye da haramcin muzguna musu, kamar haka:
(i) Da farko a babin bayanin matsayin mahaifiya, ya kawo hadisin Sahabi Mu’awiyah Bn Haidah _(Radiyal Laahu Anhu)_ wanda ya tambayi Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce: Waye zan kyautata wa?
Ya ce: Mahaifiyarka.
Na sake cewa: Waye zan kyautata wa?
Ya ce: Mahaifiyarka.
Na sake faɗin cewa: Waye zan kyautata wa?
Ya ce: Mahaifiyarka.
Na maimaita cewa: Waye zan kyautata wa?
Ya ce: Mahaifinka, sannan sai kuma sauran makusanta a cikin danginka _. (Al-Adabul Mufrad: 3; Al-Irwaa’u: 837, 2170)_
Wannan ya nuna:
Cikin dukkan dangi da sauran ’yan uwa, babu wanda ya kai matsayin mahaifiya.
Wajibi ne ɗa ya kyautata wa mahaifiyarsa fiye da yadda yake kyautata wa mahaifinsa.
Ba a cire mai aure daga mara aure a nan ba, kamar yadda ba a raba ɗa namiji daga ’ya mace ba.
(ii) Sannan kuma wani mutum ya taɓa zuwa wurin Sahabi mai daraja Ibn Abbaas _(Radiyal Laahu Anhumaa),_ ya nuna masa cewa:
Ya nemi auren wata mace sai ta ƙi amincewa ta aure shi, amma da wani ya neme ta sai ta amince za ta aure shi. Ya ce saboda zafin kishinta sai ya je ya kashe ta!
Shi ne yake tambaya: Ko yana da ƙofar tuba?
Sai Ibn Abbaas _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ ya tambaye shi: Mahaifiyarka tana da rai?
Ya ce: A’a.
Ya ce: Ka tuba ga Allaah Mabuwayi Mai Girma, sannan ka ƙara kusantarsa da kyawawan ayyuka gwargwadon ikonka.
Ataa’u Bn Yasaar _(Radiyal Laahu Anhu)_ ya ce: Sai na tambayi Ibn Abbaas: Don me ka tambaye shi a kan rayuwar mahaifiyarsa?
Ya ce: Ni dai ban san wani aikin da ya fi kusantarwa ga Allaah Mabuwayi Mai Girma ba fiye da kyautata wa mahaifiya! _(Al-Adabul Mufrad: 4; As-Saheehah: 2799)_
Wannan ya nuna:
Kisan-kai babban zunubi ne daga cikin manyan kaba’irai da suke janyo wa mutum hallaka a Lahira.
Wajibi ne ga wanda ya aikata shi ya tuba, kuma ya nemi Allaah ya gafarta masa, kuma ya kusance shi da kyawawan ayyuka.
A wurin Ibn Abbaas, babban malami a cikin Sahabbai, kyautata wa mahaifiya ya fi duk wani aikin musulmi kusantarwa ga Allaah _Subhaanahu Wa Ta’aala._
Wannan kyautatawar ba ta keɓanta ga ’ya’ya maza ban da mata ba, kamar yadda ba ta keɓanta da marasa aure ban da masu aure ba.
(iii) A game da iyayen da suka zalunci ’ya’yansu, ya sake riwaitowa daga Ibn Abbaas _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ dai cewa:
ﻣَﺎ ﻣِﻦْ ﻣُﺴْﻠِﻢٍ ﻟَﻪُ ﻭَﺍﻟِﺪﺍﻥ ﻣُﺴْﻠِﻤَﺎﻥِ ، ﻳُﺼْﺒِﺢُ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻤَﺎ ﻣُﺤْﺘَﺴِﺒًﺎ ، ﺇِﻟَّﺎ ﻓَﺘَﺢَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻟَﻪُ ﺑَﺎﺑَﻴْﻦِ - ﻳَﻌْﻨِﻰ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ - ﻭَﺇِﻥْ ﻛَﺎﻥَ ﻭَﺍﺣِﺪٌ ﻓَﻮَﺍﺣِﺪٌ ، ﻭَﺇِﻥْ ﺃَﻏْﻀَﺐَ ﺃَﺣَﺪَﻫُﻤَﺎ ﻟَﻢْ ﻳﺮﺽَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻪُ ، ﺣَﺘَّﻰ ﻳَﺮْﺿَﻰ ﻋَﻨْﻪُ
Babu wani musulmin da yake da iyaye guda biyu wanda zai tashi da safe ya tafi wurinsu don neman ladan Allaah, face kuwa Allaah ya buɗe masa ƙofofi guda biyu – yana nufin: Na Aljannah -, idan kuma guda ɗaya ne, to ƙofa ɗaya ce. Kuma idan ya fusata ɗaya daga cikin iyayensa, to Allaah ba zai yarda da shi ba har sai shi ya yarda da shi.
Aka ce: Ko da sun zalunce shi?
Ya ce: Ko da sun zalunce shi! _(Al-Adabul Mufrad: 7; As-Shaikh Dokta Muhammad Luqman Assalafiy a cikin Rasshul Bard, shafi: 16 ya ce: Hasan ne saboda hanyoyinsa guda biyu)_
Wannan ya nuna:
Kyautatawa ga iyaye tilas ne a kan ’ya’ya, ko da kuwa iyayen sun zama azzalumai masu cutarwa gare su, matuƙar dai ba a cikin keta wata doka daga cikin dokokin Ubangiji ba ne.
Allaah ba ya yarda da duk wanda mahaifinsa ko mahaifiyarsa suke fushi da shi, har sai lokacin da suka yarda da shi.
Ba a keɓance ɗa namiji daga ’ya mace ba a nan, haka kuma ba a keɓance mai aure daga mara aure ba.
(iv) A wurin faɗa musu magana mai taushi da barin kausasa musu, ya kawo riwayar wani malami Taisalah Bn Mayyaas wanda ya taɓa zama tare da khawaarijawa. Shi ne ya ce:
Watarana na aikata wani zunubi wanda ba na ganinsa sai dai kawai yana daga cikin manyan kaba’irai ne! Sai na gaya wa Sahabi Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ haka. Sai ya ce: Ai wannan ba shi daga cikin kaba’irai. Su (Kaba’irai) guda tara ne:
ﺍﻟْﺈِﺷْﺮَﺍﻙُ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ، ﻭَﻗَﺘْﻞُ ﻧَﺴَﻤَﺔٍ ، ﻭَﺍﻟْﻔِﺮَﺍﺭُ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺰَّﺣْﻒِ ، ﻭَﻗَﺬْﻑُ ﺍﻟْﻤُﺤْﺼَﻨَﺔِ ، ﻭَﺃَﻛْﻞُ ﺍﻟﺮِّﺑَﺎ ، ﻭَﺃَﻛْﻞُ ﻣَﺎﻝِ ﺍﻟْﻴَﺘِﻴﻢِ ، ﻭَﺇِﻟْﺤَﺎﺩٌ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻤَﺴْﺠِﺪِ ، ﻭَﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳَﺴْﺘَﺴْﺨِﺮُ ، ﻭَﺑُﻜَﺎﺀُ ﺍﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻌﻘﻮﻕ .
Yin tarayya da Allaah, da kisan-kai, da gudu a ranar karo da maƙiya, da yi wa matar kirki ƙazafi, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da ƙetare haddi a Haram, da mai yin izgili, da kukan iyaye saboda muzgunawa.
Daga nan sai Ibn Umar ya ce: Kana tsoron shiga Wuta, kuma kana son ka shiga Aljannah?
Na ce: E, wallahi!
Ya ce: Iyayenka suna da rai?
Na ce: Mahaifiyata ce ta ke tare da ni.
Sai ya ce:
ﻓَﻮَﺍﻟﻠَّﻪِ ، ﻟَﻮْ ﺃَﻟَﻨْﺖَ ﻟَﻬَﺎ ﺍﻟْﻜَﻠَﺎﻡَ ، ﻭَﺃَﻃْﻌَﻤْﺘَﻬَﺎ ﺍﻟﻄَّﻌَﺎﻡَ ﻟَﺘُﺪْﺧِﻠَﻦَّ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔَ ، ﻣَﺎ ﺍﺟْﺘَﻨَﺒْﺖَ ﺍﻟْﻜَﺒَﺎﺋِﺮَ .
Na rantse da Allaah! In da za ka tausasa mata magana, kuma ka ciyar da ita abinci, to da kuma lallai ka shiga Aljannah, matuƙar dai ka nisanci manyan kaba’irai. _(Al-Adabul Mufrad: 8; As-Saheehah: 2898)_
Wannan ya nuna:
Yana daga cikin manyan kaba’irai ’ya’ya su takura wa iyaye har su yi kuka.
Tausasa magana ga mahaifiya da ciyar da ita da halal na daga hanyoyin samun Aljannah.
A nan ba a ce idan ’ya mace da ta yi aure ta aikata irin haka ba za ta samu sakamako irin haka ba.
(v) Sannan a babin sakayyar iyaye, sai ya kawo hadisin Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa),_ wanda ya ga wani mutum daga ƙasar Yemen yana ɗawafin ɗakin Allaah alhali yana ɗauke da mahaifiyarsa a bayansa, yana rera baitin waƙe cewa:
ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻬَﺎ ﺑَﻌِﻴﺮُﻫَﺎ ﺍﻟْﻤُﺬَﻟَّﻞُ ... ﺇِﻥْ ﺃُﺫْﻋِﺮَﺕْ ﺭِﻛَﺎﺑُﻬَﺎ ﻟَﻢْ ﺃُﺫْﻋَﺮِ
Haƙiƙa! Ni ne raƙuminta mai sauƙin-kai … Idan abin hawanta ya yi tutsu, ni ba zan yi tutsu ba.
Sai kuma ya tambayi Ibn Umar _(Radiyal Laahu Anhumaa):_ Kana ganin ko na saka mata kuwa?
Ya ce: Ina! Ai ko da nishin naƙuda guda! _(Al-Adabul Mufrad: 11; As-Shaikh Dokta Muhammad Luqman Assalafiy a cikin Rasshul Bard, shafi: 19 ya ce: Sahih ne)_
Wannan ya nuna:
Idan har goya mahaifiya a wurin ɗawafi bai isa ya biya ko da nishin naƙuda guda ba, ina kuma ga wanda bai taɓa yi mata hakan ba?!
Idan ɗa bai iya biyan nishin naƙuda guda ba, ina kuma ga sauran wahalhalun haihuwar da suka gabace ta ko suka biyo bayan haihuwar?!
Idan har ɗa namiji duk da ƙarfin jiki da na tunani da hankalinsa bai iya biyan mahaifiyarsa ba, ta yaya ’ya mace mai rauni a gidan aure za ta iya biyan mahaifiyarta?!
(vi) Sannan a babin muzguna wa iyaye sai ya kawo riwayar Sahabi Abu-Bakrah _(Radiyal Laahu Anhu)_ wanda ya ce: Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce: Ku saurara! Shin ko in gaya muku mafiya girma daga cikin kaba’irai? (Sau uku).
Suka ce: Haka ne: A gaya mana.
Ya ce:
( ﺍﻟْﺈِﺷْﺮَﺍﻙُ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻋُﻘُﻮﻕُ ﺍﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ‏) ﻭَﺟَﻠَﺲَ ، ﻭَﻛَﺎﻥَ ﻣُﺘَّﻜِﺌًﺎ ‏( ﺃَﻟَﺎ ﻭَﻗَﻮْﻝُ ﺍﻟﺰُّﻭﺭِ ‏) ، ﻭَﻣَﺎ ﺯَﺍﻝَ ﻳُﻜَﺮِّﺭُﻫَﺎ ﺣَﺘَّﻰ ﻗُﻠْﺖُ ﻟَﻴْﺘَﻪُ ﺳَﻜَﺖَ
{Tarayya da Allaah, da Muzguna wa iyaye}. Sai kuma ya zauna alhalin a da yana kishingiɗe ne: {Ku saurara! Da Maganar ƙarya}.
Bai daina maimaita ta ba, har sai da na yi burin: Ina ma da a ce ya yi shiru! _(Al-Adabul Mufrad: 15; Sahih Al-Bukhaariy: 5976, Sahih Muslim: 143)_
Wannan ya nuna:
Muzguna wa iyaye yana daga cikin manyan kaba’irai.
Shi ne ma babban kaba’iri na-biyu.
A cikin wannan ba a cire ’yar da ta riga ta yi aure ba.
Kuma ba a bambanta ɗa namiji da ’ya mace ba.
(vii) Kuma a babin hana la’antar iyaye, sai ya janyo hadisin Aliyy Bn Abi-Taalib _(Radiyal Laahu Anhu)_ wanda ya ce: Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:
( ﻟَﻌَﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦْ ﺫَﺑَﺢَ ﻟِﻐَﻴْﺮِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ، ﻟَﻌَﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦْ ﺳَﺮَﻕَ ﻣَﻨَﺎﺭَ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ، ﻟَﻌَﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦْ ﻟَﻌَﻦَ ﻭَﺍﻟِﺪَﻳْﻪِ ، ﻟَﻌَﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻣَﻦْ ﺁﻭَﻯ ﻣُﺤْﺪِﺛﺎً )
Allaah ya la’anci duk wanda ya yi yanka domin wanin-Allaah, kuma Allaah ya la’anci duk wanda ya sace alamun kan ƙasa, kuma Allaah ya la’anci duk wanda ya la’anci mahaifansa, kuma Allaah ya la’anci duk wanda ya bai wa maɓarnaci mafaka. _(Al-Adabul Mufrad: 17; Sahih Muslim: 44)_
Wannan ya nuna:
La’anar Allaah ta tabbata a kan duk wanda ya la’anci mahaifinsa ko mahaifiyarsa.
Yana daga cikin haka ya sa wani ya la’ance su, kamar in ya fara la’antar mahaifan wancan.
A nan ba a bambanta ɗa namiji daga ’ya mace, mai aure ko mara aure ba.
(viii) Kuma a babin wanda ya riski iyayensa amma bai shiga Aljannah ba, sai ya kawo hadisin Abu-Hurairah _(Radiyal Laahu Anhu)_ daga Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce: An turmutsa hancinsa! An turmutsa hancinsa!! An turmutsa hancinsa!!!
Suka ce: Ya Manzon Allaah! Wanene shi?
Ya ce: Wanda ya riski iyayensa guda biyu a lokacin tsufansu, ko kuma ɗayansu, amma kuma ya shiga Wuta a Lahira. _(Al-Adabul Mufrad: 21; Sahih Al-Bukhaariy: 5976, Sahih Muslim: 9-10)_
Wannan ya nuna:
Rayuwa da tsoho ko tsohuwa wata babbar ƙofar alheri ne ko kuma na sharri.
Duk wanda bai yi amfani da wannan daman ba, ya shiga-uku, ya wulaƙantu.
Ba a rarrabe mai aure da mara aure daga cikin ’ya’ya maza da mata ba a nan.
(ix) Sannan a babin addu’ar iyaye, sai ya kawo hadisin Abu-Hurairah _(Radiyal Laahu Anhu)_ ya ce: Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:
( ﺛَﻠَﺎﺙُ ﺩَﻋَﻮَﺍﺕٍ ﻣﺴﺘﺠﺎﺑﺎﺕٌ ﻟَﻬُﻦَّ ، ﻟَﺎ ﺷَﻚَّ ﻓﻴﻬﻦَّ : ﺩَﻋْﻮَﺓُ ﺍﻟْﻤَﻈْﻠُﻮﻡِ ، ﻭَﺩَﻋْﻮَﺓُ ﺍﻟْﻤُﺴَﺎﻓِﺮِ ، ﻭَﺩَﻋْﻮَﺓُ ﺍﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﻋَﻠَﻰ ﻭَﻟَﺪِﻫِﻤَﺎ )
Addu’o’i guda uku ana amsa su, babu ko shakka a cikinsu: Addu’ar wanda aka zalunce shi, da addu’ar matafiyi, da mummunar addu’ar iyaye a kan ɗansu. _(Al-Adabul Mufrad: 32; Saheehah: 596)_
Wannan ya nuna:
Allaah yana amsa mummunar addu’ar da iyaye suka yi wa ’ya’yansu mai kyau ko mara kyau.
Wajibi ne ’ya’ya su guji aikata duk abin da zai janyo musu samun mummunar addu’ar iyaye.
Ba a ce sai ’ya’ya maza kawai ban da mata ba, kuma ba a ce ’ya’ya marasa aure kawai ban da masu aure ba.
A taƙaice dai, har a bayan aure haƙƙoƙin iyaye ba su sauka daga kan ’ya’yansu maza da mata ba. Don haka wajibi ne ’ya’yan su cigaba da bayar da waɗannan haƙƙoƙin ga iyayensu da gwargwadon ƙarfinsu da ikonsu, kamar yadda suke bayar da haƙƙoƙin da suke kansu dangane da junansu a gidan aure.
Kuma su yawaita addu’o’in alkhairi ga kansu da iyayensu, Allaah ya sa idan mai rabawa ta zo, ta raba su lafiya ba tare da fushin iyaye a kansu ba.
Sannan kuma a duk lokacin da aka samu saɓani a tsakanin umurnin iyaye ko na miji a nan ne ake cewa mace ta gabatar da umurnin miji a kan na iyayenta, kamar yadda muka yi bayani a cikin littafin *Iyaye ko Miji?*
Amma shi namiji bai halatta ya gabatar da ra’ayin matarsa a kan na mahaifiyarsa ba, kamar kuma yadda bai halatta ya fifita ra’ayin mahaifinsa a kan na mahaifiyarsa a lokacin da suka samu saɓani ba.
_Wal Laahu A’lam._
_Wa Sallal Laahu Wa Sallama Wa Baaraka Alaa Nabiyyinaa Muhammadin Wa Alihi Wa Sahbih Wa Ikhwaanih._
Daga:
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy,
_Markazu Ahlil-Hadeeth_ ,
Post a Comment (0)