FALALAR YIN AZUMI DOMIN ALLAH



FALALAR YIN AZUMI DOMIN ALLAH

_*Daga Zauren:*_
_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_

_Bismillahir Rahmanir Raheem._

_عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: قال رسول الله ﷺ: *«ما من عبد يصوم يوماً في سبيل الله إلا باعد الله بذالك اليوم عن وجهه النار سبعين خريفا».* متفق عليه، واللفظ لمسلم._

_An kar6o daga Abi Sa'idul Khudry (r.a) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: *«Babu wani bawa da zai azumci yini daya domin Allah, face Allah Ya nisanta fuskarsa na daga wannan yinin daga wuta da yanki saba'in».* Bukhary da Muslim, amma lafazin Muslim ne._

_'Yan uwa a taqaice, wannan hadisin na kwadaitar da mu ne game da yin azumi domin Allah, ba don riya ba ko nuna gwaninta ko burge Wani._

_Azumi na sa a nisanta bawa daga wuta, amma fa wanda ya yi shi domin Allah._

_Don haka 'yan uwa mu dage da yin azumi domin Allah domin mu samu dacewa da irin bayin da azumi ze ceta a ranar Lahira._

_Ya Allah Ka kare mu daga wuta 🔥👏🏽_

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)