Mace ce Mijinta yasadu da'ita amma kafin tayi wanka sai Haila tazo mata, Shin wanka biyu zatayi kenan ko yaya?



TAMBAYA❓

Mace ce Mijinta yasadu da'ita amma kafin tayi wanka sai Haila tazo mata, Shin wanka biyu zatayi kenan ko yaya?

AMSA👇

_*Alal-Haƙiƙa* ansamu *Saɓānin Mālamai* dangane da hukuncin Matar da tasadu da Mijinta kokuma tayi mafarki amma kafin tayi *Wankan-Janaba* sai *Jinin-Haila* yazo mata, kokuma yakasance Mace tana cikin *Jinin-Hailarne* kuma sai tayi mafirki har Maniyyi yafito mata,_
:
_*Mazhabin Hanābila* dakuma wasu daga cikin *Mālamai* suntafi akan cewa ba wajibi bane akanta tayi sai tayi *Wankan-Janaba,* danhaka zata jirane harsai *Jinin-Hailar* yaɗauke sannan tayi wanka, amma inda zatayi *Wankan-Janabar* alokacin datake *Jinin-Hailar,* shikenan wankanta yayi kuma hukuncin janaba yasauka daga kanta, shikuma *Jinin-Hailar* hukuncinsa yana tare da'ita harsai idan ya yanke sai tayi masa wanka, amma idan batayi *Wankan-Janabarba* harsaida *Jinin-Hailar* yaɗauke mata, mafi yawan *Mālamai* waɗanda suka haɗa harda *Mazhabobin nan guda huɗu sanannu,* suntafine akan cewa idan tazo wankan zata ƙulla niyyar *Wankan-Janaba* da *Wankan-Haila* azuciyarta saitayi wanka guda ɗaya ya wadatar, amma wasu daga cikin *Mālamai* suntafine akan cewa dolene sai tayi wanka biyu kowanne nasa dabam, saidai maganar farko da'akace zatayi wanka ɗayane da niyya biyu tafi inganci,_
:
_Amma *Mazhabin Mālikiyya dakuma Hanābila* sukace idan da zata ƙulla niyyar *Wankan-Janaba* kaɗai azuciyarta ko *Wankan-Haila* kaɗai, to iya abinda ta *ƙulla niyyar* akansane kawai yagushe daga gareta banda ɗayan, domin *Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ)* Yace:_
:
*"إنما الأعمال بالنيات، وإنما لكل امرئ ما نوى"*
*_MA'ANA:_*
*_Lallai ayyuka (na ibada) saida niyya, kuma kowanne mutum (ana karɓar aikin) da yayiwa niyya ne,_*
:
_Saidai *Mazhabin Shāfi'iyya da Hanafiyya* sukace koda niyyar wanka guda ɗaya kaɗai ta ƙulla azuciyarta sukace yayi saboda zai iya ɗauke hukuncin ɗaya wankan, to amma maganar *Mālikiyya da Hanābila* tafi inganci dakuma Dalili mai ƙarfi,_
:
_Danhaka magana mafi inganci wacce mafi yawan *Mālamai* suka tafi akanta shine, idan *Jinin-Haila* yazowa mai Janaba kokuma Janaba tazowa mai Haila, to zata dakatane harzuwa lokacin da *Jinin-Hailar* zai ɗauke mata, sai ta ƙulla niyyar *Wankan-Janaba* da *Wankan-Haila* azuciyarta sai tayi wanka guda ɗaya ya isar mata,_
:
(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαппαп ʟıттαғı καмαя нακα:
"المغني لإبن قدامة" (1/135)

     AMSAWA
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505

_Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana._ 

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)