MUNYI SALLAH ACIKIN ZAURE???
.
.
*Tambaya ta 7,399:*
=
Mune mukaje sallar juma'a, to wuri ya cika sosai sai zauren wani gida dayake bakin titine wajen sai muka shige mukayi sallah a ciki. Sai wani yace bamuda da sallah. shin ya abin yake shin sallar mu tayi??
Sannan Kuma babu kyau yin sallar juma'a a zauren gidan mutane??
=
=
Amsa
=
_Idan har abun haka yake kamar yadda kafaɗa toh sallarku tayi. Domin asali wajibine a daidaita sahu kuma ayi sallah acikin masallaci acikin sahu wannan asalinsa wajibine. Idan har akwai waje acikin masallaci ko a haraba se kukaƙi shiga masallacin kokuma kukaƙi shiga harabar kuka zauna anan waje ko zauren can kukayi sallar toh a wannan halin bakuda sallah. Amma idan babu wajene acan cikin masallaci babu waje a haraba shine yasa kuka tsaya anan wannan zauren kukayi sallah toh wannan kunada uziri kuma sallarku tayi insha Allahu, domin idan akace ba'a yarda kuyi sallar anan zaurenba toh inane inda akeso kuje kuyi sallar????_
=
=
Allah Yasa mudace
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
09031200070
.
°
Yau
09-02-1443
17-09-2021
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
Domin samun shafinmu a Telegram
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
°
Kuna iya samun tsoffin darussanmu kai tsaye ta cikin wannan shafin
http://zaurenkitabuwassunnah0.blogspot.com
.
*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ اللهم ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ*
.
*Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illa anta astagfirukallahumma wa atubu ilaika*