NA YI MAFARKIN JIMA'I AMMA BAN GA MANIYYI BA



NA YI MAFARKIN JIMA'I AMMA BAN GA MANIYYI BA

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum. Barka da safe tambayata ita ce Idan mutum ya yi mafarki ko da bai ga komai a jikinsa ba dole ne sai ya yi wanka?

*AMSA*👇

Wa'alaikumus Salam. Wanda ya yi mafarkin saduwa, idan ya farka ya duba tufafinsa bai ga alamar ya fitar da maniyyi ba, to ba zai yi wanka ba, saboda hadisin Ummu Salamata da ta ce: Ummu Sulaimin matar Abu Dalha ta zo wurin Manzon Allah ï·º.

Sai ta ce masa: Ya Manzon Allah, lallai Allah ba ya jin kunyar faÉ—in gaskiya, shin wanka ya wajaba a kan tamace idan ta yi mafarki? Sai Manzon Allah ï·º ya ce: "E, amma idan ta ga ruwa". A nan idan ta ga ruwa yana nufin idan ta ga maniyyi.
Bukhariy 130, Muslim 313.

Wato dai idan mutum ya yi mafarkin jima'i sai bayan da ya farka ya duba tufafinsa bai ga alamar maniyyi ba, to wanka ba ta hau kansa ba.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.* 

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)